FARFESA HABU MUHAMMAD, fitacce ne a Jami’ar Bayero da ma sauran jami’oin gida da na waje, mutun ne mai kishin ganin an inganta tsarin Dimokuradiyya, da kyakkyawan shugabanci a Nijeriya baya ga zamowar sa cikin masu kyakyawar fahimta a kan al’adu da harshen Hausa.
Watanni biyu da suka gabata, ya zama shugaban cibiyyar nazarin kimiyyar siyasa da ke gidan tunawa da marigayi Malam Aminu Kano, wanda aka fi sani da Gidan Mumbayya da ke karkashin Jami’ar Bayero ta Kano.
- Da Dumi-Dumi: Dan Takarar Gwamna Ya Rasu A Adamawa
- An Yi Girgizar Kasa Mai Karfin Maki 5.6 A Gundumar Luding Ta Lardin Sichuan Na Kasar Sin
Wakilinmu MUSTAPA IBRAHIM KANO ya tattauna da shi kan akidar siyasar Malam Aminu Kano, daya daga cikin mazan jiya ‘yan gwagwarmaya, da kuma ta ‘yan siyasar wannan zamanin.
Har ila yau da sauran wasu al’amura da aka bullo da su a cibiyar wanda za a rika gabatarwa da harshen Hausa zalla, ga dai tattaunawar kamar haka:
Da farko za mu so ka gabatar da kanka…
Sunana Farfesa Habu Muhammad, ni ne Babban Darakta ko kuma in ce, Shugaban Cibiyar Nazarin Kimiyyar Siyasa, da ke Gidan tunawa da Malam Aminu Kano, wato Gidan Mumbayya, da ke karkashin Jami’ar Bayero ta Kano. Na zama Daraktan wannan cibiya ne a ranar 6 ga Oktoban 2022. Hakan ta kasance ne bayan mutumin da na gada Farfesa Zango ya kammala wa’adin aikinsa na jagorancin gidan da ke Unguwar Gwammaja, a Karamar Hukumar Dala.
Farfesa, me ka fara da shi yayin da ka sa kafa a wannan cibiya a matsayin daraktanta?
To, Alhamdu lillahi bayan na samu mukamin shugaban ita cibiyar kamar yadda na yi bayani a baya, abin da na fara yi, duk da yake ni ba bako ba ne ba a Jami’ar Bayero, an san ni kamar yadda na san kun san da hakan, shi ne na gabatar da kaina ga hukumomi da kungiyoyi har ma da fadar mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero. Na ziyarci shugabanmu wanda shi ne shugaban hukumar gudanarwa ta wannan gida da mukaddashin shugaban Jami’ar Bayero ya nada wato Farfesa Hafizu Abubakar Tsohon Mataimakin Gwamnan Kano. A cikin wadanda na ziyarta har da shugaban kungiyar kiristoci ta kasa (CAN) Rabaran Namaza Merry, sauran wuraren da na ziyarta sun hada da kafofin yada labarai kamar NTA, Freedom Rediyo Jalla Rediyo da dai sauran kafofin yada labarai da ke Kano.
Bugu da kari kuma, yanzu haka ina kokarin ziyartar mai girma Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, duk da halin dinbin ayyukan da suke gabansa, amma dai ziyarar har yanzu ba ta yiwu ba, amma da ikon Allah har yanzu ana sa ran kai masa ziyarar. Dalili kuwa shi ne na karbi shugabancin Gidan Mumbayya ne a dai-dai lokacin da ake hada-hadar siyasa da kusantowar zabe, wanda ana bukatar hadin kai da gudunmawar kowa don samun nasarar ingantaccen zabe wanda kowa zai amince da yadda aka gudanar da shi. Akwai maganar Dimokuradiyya wacce za ta ba da shugabanci nagari a kasa, da kuma matakan Jihohi, da kananan hukumomi domin bunkasar tattalin arziki mai yawa a kasarmu Nijeriya.
Bayan ita ziyarar, an yi taro wanda na fara shugabanta a wannan gida wanda shi ne aka yi a ranar 1 ga Nuwambar 2022, da aka yi addu’ar tunawa da Farfesa Dalhatu Shehu, daya daga cikin wadanda suka jagoranci wannan cibiya ta Gidan Mumbayya a shekarun da suka gabata, Allah ya jikansa ya rahama masa.
Bayan wanna kuma an tattauna hanyoyin da za a bi don ganin an tabbatar da an ba kananan hukumomi ‘yancin cin gashin kansu na maganar kudadensu su rika zuwa asusunsu kai tsaye, yadda za a samu ci gaba ta hanyar rage matsaloli a matakan kananan hukumoni da dai sauransu.
Farfesa bari mu dan yi waiwaye adon tafiya, ko za ka dora akidar siyasar Malam Aminu Kano da ta ‘yan siyasar yau a mizani?
To ita siyasa irin ta su Malam Aminu Kano siyasa ce ta a kida ta a `yantar da talaka daga kangin bauta da wulakanci da ake wa talaka a wancan lokacin, kuma siyasa ce ta neman `yanci domin sun san, ko mene ne ‘yanci domin ko ba komai sun yi gwagwarmaya da gumurzu na shan wahala da suka samu daga turawan mulkin mallaka kan maganar `yanci. To ka ga wasu daga cinkin su ko su Malam Aminu Kano suna da wannann ilimin kuma suna da wannan ruhin na neman `yanci cikin wahala da azaba da matsaloli daban-daban.
Saboda haka za ka ga siyasar su Malam Aminu Kano siyasa ce ta neman `yancin talaka, da `yantar da shi daga kangin bauta da za ka iya cewa masu gudanar da mulki na wancan lokacin sun sa talaka a kangin bauta, haka ne ma ya sa su Malam Aminu Kano da sauran `yan siyasar zamaninsa suke da wani take na SAWABA-SAWABA, to abin da suke nufi a wancan lokacin nasu shi ne irin abin da suke wa talaka na karbar haraji, da jangali, da sa mutum noma a gonar Rogo, ko makamancin haka ba tare da an biya shi ba, to wannan da wasu abu masu kama da wannan shi ne abin da su Malam Aminu Kano suka yi yaki da shi a tafiyarsu ta NEPU da PRP kuma wannan za ka ga cewa ita ce a kidar su Malam Aminu Kano da sauransu.
Kuma har ila yau wani abin lura, su, su Malam Aminu Kano babu batun tara kudi a akidar su illa dai kawai `yancin talaka, da biya masa bukata daidai gwargwadon iko, ka ga babu maganar cin hanci da rashawa da almundahana amma na yanzu mafiyawa daga cikinsu ko 99 bisa 100 suna kokarin tara abin duniya ne har ma ya fi karfin bukatarsu ta rayuwa. To saboda haka a takaice akidar siyasar Malam Aminu Kano ta sha bamban nesa ba kusa ba da `yan siyasarmu na yau.
Bambanci ko kuma in ka kwatanta da `yan siyasar yanzu a kasin haka ne, wato su ‘yan siyasar yanzu ba su san ma mene ne `yanci ba, abin da suka sani shi ne tara kudi dan amfanin kansu da `ya`yansu, da matansu, da wadanda suke so su azurta, saboda haka idan ka kwatanta siyasar su Malam Aminu Kano da `yan siyasar yau abin ya sha bamban nesa ba kusa ba saboda canjin zamani da canjin yanayin.
Kasancewar Malam Aminu Kano na da daliban siyasa ko mabiyansa da suka saura, ko a cikinsu akwai wadanda kake ganin suna kan akidar siyasa irin tasa a yanzu?
To a gaskiya dalibai ko mabiya siyasar Malam Aminu Kano ko wadanda suka kasance abokan siyasarsa da su kai saura kalilan ne, daga cikinsu idan ma suna raye, domin ko daliban siyasarsa da za ka kira mabiyansa to a wannan lokaci matasa ne kuma kadan ne suke cikin siyasa domin yanayi na zamani ko dai ba su da tasiri a cikin siyasar ko kuma sun hakura da yanayin da suke gani ta rashin manufa da dacewa da akidun NEPU da PRP kuma wadanda ma suka yi har suka rike mukamai manya a gwamnati sun dai kwatanta abin da za su iya amma dai ba su da yawa.
Haka kuma idan ma ka duba su jam`iyyun da dalibai ko mabiya Malam Aminu Kano da suka saura suka shiga a yanzu, za ka ga cewa ba jam`iyyu ne ba na manufar gina talaka ba, jam`iyyu ne na `yan jari hujja kuma za ka ga cewa ko wadanda suka debi kudi a gwamnati ko wadanda suka kafa jam`iyyun kuma ba ka da wata dama da za ka yi abin da za ka yi sai abin da ya dace da son ransu. Magana ce ta kudi saboda haka ne abubuwa suka canza nesa ba kusa. Haka kuma za ka ga ko da `yan majalisa ne, ko na tarayya ne, ko sanatoci ne za ka ga dai cewa magana ce dai ta a nemo kudi daga Abuja, kuma rashin akidar ne za ka ga idan an zabi mutum ya tafi ba za ku kara ganinsa ba, sai zabe ya zo kuma rashin a kidar ce ta siyasa za ka ga cewa yau mutum yana wannan jam`iyya gobe kuma yana wancan jam`iyya ana juya su kamar waina.
Har ila yau akwai wadanda suke amfani da sunan koyi da Malam Aminu Kano amma a baki ne kawai ba a zuciya ba kuma suna amfani da wannan domin cimma burinsu na siyasa amma gaskiya ba akidar malam ce da su ba, domin kamar yadda na gaya ma wasu mabiyan sun kwatanta, wasu ba su ma kwatanta ba kuma ko ka shiga da akidar, to za ka ga cewa dai kawai ba wannan maganar ba ce ana ma ingiza-mai-kantu-ruwa ne, kawai dai ka samo kudi ka ba su shi ne magana.
Dan haka a nan Munbayya House akwai taro tunawa da ake yi duk shekara ana gayyato dattawa da sauran masana wanda suka yi zamani da Malam Aminu Kano suna baje kolinsu, a nan ma za ka samu bayanai na rayuwar Malam Aminu Kano daban-daban na kishinsa da talaka, da sauran tarurruka irin na kafuwar NEPU dan jin tarihin magabatan shugabanni da sauran `yan gwagwarmayar tabbatar da `yancin talakawa da sauransu.
A halin yanzu akwai wani abu da kuka shirya aiwatarwa da ya shafi dimokuradiyya a wannan gida?
Na zo da shiri ko tsari na aiwatar da abubuwa, to abu ne da za ka iya cewa kamar dori ne daga wurin da wanda na gada ya tsaya, wato Farfesa Zango, amma dai ni abin da na zo da shi, daga ciki akwai wanda na yi wa take da ‘Dimokuradiyya A Yau’, wani shiri ne, da za a rika gayyato masana su zo su gabatar da kansu da gabatar da jawabi. Jawabi a kan wasu matsaloli da suke damun jama’a domin a samu damar warware masu abubuwan da suka sa suka shiga duhu, ba ma kamar damukuradiyya da sauran matsaloli masu yawa, da kawo abubuwan da za su kawo wa jama’a ci gaba, ta kowanne fanni na rayuwa, shi ne abu na farko.
Ga kuma taron fadakarwa a wannan cibiya wanda ya kunshi kiran ‘yan takara na gwamnoni, amma ba muhawara ta keke-da-keke ce za a yi ba, ba kamar yadda aka saba yi a baya ba. Ita wannan gayyato dan takara za mu yi ne don ya zo ya yi bayani da kansa, sannan in da akwai tambayoyi daga mahalarta taron sai su yi masa. Tsarin namu ya yi nisa domin yanzu mun raba takardun gayyata ga ‘yan takarar gwamnoni, kowa shi zai ba da rana da lokacin da zai zo, ya yi da kansa. Haka su ma a matakan ‘yan takarar shugaban kasa shi ma haka muka tsara, shi ma dan takarar shugaban kasa zai zo ya yi bayani manufofunsa da abin da ya tsara wa al’ummar kasa duk dai da mun san halin da ake ciki na hada-hadar yakin neman zabe, kamar yadda ake cewa a yanzu da dai sauransu. Kuma a wannan shiri babu wani tsari ko shiri na nuna bambanci ga wata jami’iyya ko wani shugaban jam’iyya cikin 16 ko 18 da ake da su a Nijeriya.
Haka nan ma akwai abin da muke kira zauren Gidan Mumbayya, wanda ake cewa ‘Munbayya Academy forum’, shi wannan shiri ne wanda za mu gayyato Malaman jami’oi da muke da su a nan Kano kamar Jami’ar Bayero, JamI’ar Wudil, da kuma Jami’ar Maitama Sule, Malamin da ya zo, zai yi jawabi ne a kan wani bincike, ko wani bayani da zai amfani masana, da sauran al’umma, za mu fara wannan shiri na MAF a wannan shekara in Allah ya so.
Abu na uku shi ne da nake son yi a wannan cibiya ta nazarin kimiyar siyasa shi ne abin da ake kira zauren tattaunawa da al’umma wanda za a gayyato masana a kan fannoni daban- daban, da sauran masu ruwa da tsaki dan tattauna wasu matsaloli da suka shafi jama’a. Matsalolin a kan shugabanci ne wato siyasa, kasuwanci ne, aure ne, harkar sufuri ce, harkar da ta shafi al’amuran yau da kullum ce da dai sauransu. Duk za a zo a tattauna matsalolin da suka damu al’umma domin gano bakin zare na warware matsalar a daidai wannan lokaci kuma a wannan zaure. Za mu fadada shi, ga mutanen gari, da Gidan Mumbayya zai rika shiryawa don warware matsaloli da Hausa za a gabatar domin la’akari da tasirin da Hausa take da shi a halin da ake ciki, na masu amfani da ita a kafofin yada labarai kamar Jaridun Hausa, gidajen Rediyo da sauran makamantansu.
Haka nan a harkar kasuwanci ta yau da kullum kowa ya san Hausa na da tasiri ana gane abubuwa sosai fiye da yadda mutane suke tunani, domin in an lura za a ga cewa masu amfani da Hausa a yau, a nan yankin sun fi masu jin turanci yawa, dama ai bukatar maje Haji ai Sallah ce.
Manufarmu ita ce a gane ba nuna turancin muke bukata ba, a nan ka ga in aka yi da Hausa masu jin Hausa da Turanci za su gane, wadanda ba su sha’awa ko jin Turancin ma za su gane, ka ga bukata ta biya ke nan, a wannan Zaure da muke kira da suna ‘Town Hall’.
Farfesa, wacce rawa jaridun Hausa za su taka wajen samun nasarar wadannan sabbin tsare-tsare?
To bisa la’akari da yadda muka lura da cewa kafofin yada labarai na Hausa da jaridun Hausa suna da dinbim makaranta da masu bibiyarsu babu shakka, haka za mu hada kai da Jaridun Hausa sosai domin isar da sako a lungu na birni da karkara, ba ma kamar mutanenmu da suke kudancin kasar nan da ma sauran wasu wurare suna bibiyar jaridun Hausa da sauransu. Yanzu ana bibiyarmu ma ta hanyar kafofin sadarwa na zamani, to wannan abu ne da za mu yi iya kokarinmu mu ga mun hada kai da duk wata kafa da sakonmu zai isa duk inda ake bukata gwargwadon hali.
Ana yin hakan ne domin al’umma su rika samu suna karantawa a kokarin da muke na wayar da kan al’umma ta kowanne fanni, har ma da abubuwan da suka shafi turanci shi ma sai an yi da shi, duk da yake mu dai burinmu shi ne masu jin Hausa a ba su damarsu ta karantawa da Hausa da kuma saurare da sauransu, burinmu dai shi ne mu ilmantar da al’umma masu jin Turanci da masu jin Hausa zalla, a wannan cibiya ta nazarin kimiyyar siyasa ta Gidan Mumbayya.
Haka nan muna da dangantaka ko alaka kyakkyawa da kafofin yada labarai na Talbijin, da Rediyo dake nan Kano da muke gabatar da shirye-shirye, a kullum so ake a fadi wani abu domin yada ilimi cikin duniya ta wadanan kafofi.
Ku kuna da alaka da wasu cibiyoyi don yada ilimi da sauran abububuwan da za su amfani al’uma?
Kasancewar Gidan Mumbayya manufa gidan tunawa da marigayi Malan Aminu Kano ya kai kimanin shekaru 25 zuwa 30, haka ne babu tantama, muna da alaka da kungiyoyi, hukumomi, daban-daban don hada kai da ciyar da jama’a gaba, kungiyoyi da cibiyoyi na gida da na waje, kamar yadda doka ta tsara. Misali; akwai kyakkyawar alaka tsakaninmu da Gidauniyar Mukta, da dai sauransu, har a kasashen Turai da ma sauran hukumomi na gida.
Kuma kamar yadda na gaya ma a baya cewa ana dab da yin zabubbuka a matakai daban- daban a Nijeriya don yanzu haka muna kokarin gayyatar hukumar zabe INEC, hakan zai sa a samu bayanai daga wurinsu domin jin matsayinta a kan shirye-shiryenta na zabe, da dai sauran abubuwa wadanda za su kawo ci gaban al’umma daidai da muradin wannan cibiya ta Mumbayya wadda Jami’ar Bayero ta kafa don kawo ci gaban al’umma.
A karshe mene ne sakonka ga jama’a?
Sako na ga al’umma da sauran masu ruwa da tsaki na kusa da kuma na nesa, da sauransu a taya mu da addu’a da hadin kai, muna kuma bukatar shawarwari masu amfani daga ko ina wadanda za su taimaka wajen ci gaban al’umma ta kowacce fuska, mai amfani don samun ilmi da wayewa a tsakanin al’umma ana bukatar gudunmawar kowa domin samun alkahairi a Kano da ma kasa baki daya.