Majalisar Dokoki ta Ƙasa (NASS) ta yi gargaɗin cewa idan ba a yi taka tsantsan ba, matsayinta na bashin gwamnati, wanda ya kai Naira tiriliyan 149.39 daidai da Dala biliyan 97 a kwata na farko na shekarar 2025, na iya haifar da haɗari ga makomar ƙasa.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da Shugaban Majalisar Wakilai, Hon. Abbas Tajudeen, ne suka yi wannan gargaɗin a taron shekara-shekara na 11 na Ƙungiyar Kwamitocin Binciken Asusun Jama’a ta Yammacin Afirka (West Africa Association of Public Accounts Committees – WAAPAC) da aka gudanar a Abuja jiya.
- Akpabio Da Abbas Sun Yi Gargaɗi Kan Ciwo Bashi Ba Tare Da Sa Ido
- Gwamnatin Tarayya Ta Gurfanar Da Natasha A Kotu Kan Zargin Ɓata Sunan Akpabio Da Yahaya Bello
Akpabio, wanda Sanata Osita Izunaso ya wakilta, ya bayyana cewa rashin kulawa da bashin gwamnati na iya sanya makomar ƴan ƙasa cikin haɗari kuma ya raunana dimokuraɗiyya a faɗin Yammacin Afirka. Ya ce idan aka sarrafa bashin yadda ya kamata, zai zama muhimmin aiki wajen ɗaukar nauyin ayyukan more rayuwa da ci gaban ɗorewa. Amma idan aka bar shi ba tare da sanya ido ba, zai zama nauyi mai haɗari.
A nasa ɓangaren, Abbas ya bayyana damuwa cewa basussukan Nijeriya sun kai wani matsayi mai hatsari. A cewarsa, jimillar basussukan gwamnatin Nijeriya ya kai Naira tiriliyan 149.39 (kimanin Dala biliyan 97) a zangon farko na shekarar 2025, wanda ya nuna ƙaruwar da ta fi na shekarar da ta gabata. Ya ce bashin da ya kai kusan kashi 52 cikin 100 na GDP ya zarce iyakar kashi 40 cikin 100 da doka ta ƙayyade.
Abbas ya ce: “Wannan karya haddin bashi ne, kuma wata alama ce ta matsin lamba ga tattalin arzikin ƙasa. Hakan ya nuna gaggawar buƙatar ƙarfafa sa ido, yin aro cikin gaskiya da bayyana dukkan bayanai, da kuma tabbatar da cewa kowace Naira da aka aro ta samar da amfanin tattalin arziki da zamantakewa.”
Ya ƙara da cewa a faɗin Afirka, bashi ya zama babban ƙalubale ga tattalin arziki, inda ƙasashe da dama ke kashe fiye da kuɗin kiwon lafiya wajen biyan bashin da suka ci. Ya ce kashi 35 cikin 100 na bashin ƙasashen Turai na daga masu ba da rance masu zaman kansu ne, kashi 39 daga ƙungiyoyin haɗin gwiwa irin su IMF da Bankin Duniya, kashi 13 daga ƙasashen da ke bayar da rance kai tsaye, yayin da kashi 12 daga Ƙasar China.
Abbas ya bayyana cewa Nijeriya ta kuduri aniyar jagorantar kafa tsarin duba bashin ƙasashen Yammacin Afirka ƙarƙashin WAAPAC, domin daidaita rahotanni, samar da ƙa’idojin gaskiya da bayyana bayanai, tare da bai wa majalisu damar samun bayanai cikin lokaci don inganta bincike.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp