Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya sanar da kafa kwamitin shugabannin riko na majalisar, domin gudanar da wasu ayyuka.
Sanarwan kwamitocin da aka dade ana jira ta zo ne jim kadan bayan kammala harkokin yau da kullum bayan tabbatar da nadin ministoci 45 daga cikin 48 da shugaba Bola Tinubu ya mika mata.
- Yadda Rufe Sararin Samaniyar Nijar Zai Shafi Sufurin Jiragen Sama A Yammacin Afirka
- Saudiyya Ta Jagoranci Zaman Sulhu Tsakanin Rasha Da Ukraine
Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan ne zai jagoranci kwamitin tsaro; Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Sanata Aminu Tambuwal ne ke jagorantar kwamitin gidaje, kuma tsohon gwamnan jihar Edo, Sanata Adams Oshiomhole ne zai jagoranci kwamitin cikin gida.
Sauran sun hada da Sanata Godiya Akwashiki (Rundunar Sojin Sama); Sanata Fatai Buhari (Jigilar Jiragen Sama); Sanata Osita Izunaso (Kasuwacin Cikin Gida); Sanata Seriake Dickson (Kula da Yanayin Hallitu); Sanata Jide Ipisagba (Harkar Man Fetur); Sanata Aliyu Wadada (Asusun Jama’a); Shehu Kaka (Ayyuka na Musamman); Sanata Patrick Ndubueze (Aiki); Sanata Solomon Adeola Olamilekan (Kasuwanci); Sanata Sani Musa (Harkar Kudi), da Sanata Tokunbo Airu (Banki).
Haka kuma, wadanda za su jagoranci kwamitocin majalisar dattawa sun hada da Sanata Adamu Aliero (Sufurin kasa); Sanata Gbenga Daniel (Sojin Ruwa); Sanata Barinada Mpigi (Yankin Neja Delta); Sanata Mohammed Monguno (Ma’aikatar Shari’a); Sanata Yemi Adaramodu (matasa da wasanni); Sanata Ireti Kingigbe (Al’amuran Mata); Sanata Orji Kalu (Ma’aikatu Masu Zaman Kansu); Sanata Mustapha Sabiu (Harkar Noma); Sanata Aliyu Ikra Bilbis (Sadarwa), da Sanata Asuquo Ekpenyong (NDDC).
Yayin da Sanata Isa Jubril zai jagoranci kwamitin kwastam; Sanata Elisha Abbo (Al’adu da yawon bude ido); Sanata Victor Umeh (Jama’a); Sanata Lawal Usman (Ilimi); Sanata Yunus Akintunde (Muhalli); Sanata Ibrahim Bomai (Birnin Tarayya); Sanata Sani Abubakar (Ma’aikatar Harkokin Waje); Sanata Harry Banigo (Lafiya); Sanata Abdulazeez Abubakar Yari (Tsarin Ruwa); Sanata Enyinaya Abaribe (Wuta), da Aliyu Magatakarda Wamakko (Bashin cikin gida da waje).
LEADERSHIP ta ruwaito cewa tun da farko shugaban majalisar dattawa ne ya kafa wasu kwamitoci saboda muhimmancin da suke da shi a harkokin yau da kullum na majalisar.