• English
  • Business News
Thursday, September 18, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Akwai Alamun Ba Gudu Ba Ja Da Baya A Kan Batun Taiwan

by CMG Hausa
3 years ago
in Daga Birnin Sin
0
Akwai Alamun Ba Gudu Ba Ja Da Baya A Kan Batun Taiwan
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Hausawa dai na cewa: “komai nisan jifa, kasa za ta dawo”. A nan ina ma nuni da batun Taiwan a kan cewa ko ba dade, ko ba jima, Taiwan za ta dunkule ko kuma za ta hade da jamhuriyar jama’ar kasar Sin, kasancewar Taiwan wani yanki ne karkashin kasar ta Sin.

A kwanan nan ne ofishin kula da harkokin Taiwan da na watsa labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin a Beijing suka fitar da wata takardar bayani kakkarfa mai taken “batun Taiwan da dunkulewar kasar Sin a sabon zamani”. Takardar dai tana kunshe da gargadi da jan kunne ga tsirarrun ’yan aware na tsibirin Taiwan tare da masu ingiza su daga kasashen ketare musamman ma kasar Amurka.

  • Ziyarar Babbar jami’ar Lithuania A Taiwan Shirme Ne

Idan ba a manta ba a wani kokarin tada zaune tsaye da Amurka ta yi a kwanan baya a yayin da kakakin majalisar wakilan kasar Nancy Pelosi ta kai ziyara tsibirin Taiwan duk da gargadin da kasar Sin ta yi, ya kawo cece kuce da gurbata dangantaka tsakanin kasashen biyu.

A sakamakon wannan tada husuma ne ma sojojin ’yantar da jama’ar kasar Sin (PLA) suka yi wani abun da ya nuna taunar tsakuwa domin aya ta ji tsoro a yankin tsibirin na Taiwan da kewaye domin mika sako cewa kasar Sin fa ba za ta yarda da wata rashin kunya da cin mutunci a yankin da ke mallakarta ba.

Kamar yadda na saba ambatar matsayina a kan batun Taiwan, ina nanata rashin gamsuwata ga yadda wasu kasashen ketare musamman Amurka take tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin, har ma a ce a kan batun Taiwan wanda ita kanta kasar Amurka ta tabbatar da yankin na Taiwan yanki ne na kasar Sin, kuma kasar Sin daya ce tak a duniya.

Labarai Masu Nasaba

Ya Kamata A Kiyaye Nasarorin Da Aka Cimma A Shawarwarin Sin Da Amurka 

Yawan Kadarorin Kamfanoni Mallakar Gwamnatin Sin Ya Wuce Yuan Triliyan 90 a Lokacin Shirin Raya Kasa Na 14 Na Shekaru 5 

Kasar Amurkan dai ta rattaba hannu a shekarar 1978 a kan wannan batu. Bugu da kari, akwai wani kuduri mai lamba 2758 wanda aka zartas a babban zauren majalisar dinkin duniya MDD da ya tanadi manufar kasar Sin daya ce a duniya, wanda daukacin kasashen duniya sun yi ammana da shi.

Ina mai matukar jinjina ma kasar Sin da ta bugi gaba ta wallafa wannan takardar bayanin da ta nuna cewa ita fa ba kanwar lasa ba ce, kuma tana nan a kan bakanta na ganin cewa Taiwan ta dawo ta dunkule da mahaifarta a tafarkin “kasa daya, tsarin mulki biyu”.

Kamar yadda na ambata da farko, sanin kowa ne cewa tun asali Taiwan yanki ne a karkashin kasar Sin kuma mallakarta ne, wannan batu dai yana da ingantaccen tushe na tarihi da doka.

A wasu bayanai da takardar da aka watsa suka kunsa, sun nuna cewa manufar kasar Sin daya tak, na wakiltar duk matsayar kasa da kasa, kuma ta yi daidai da ka’idojin huldar kasa da kasa.

A karshe ina son jawo hankalin tsirarrun ’yan aware na Taiwan da kasashe masu zuga su da su yi hattara kuma su lura da take taken su wanda suke nuna neman tashin hankali karara a tsibirin na Taiwan.

Jama’ar Taiwan kamar yadda tarihi ya nuna Sinawa ne, ba ja in ja a nan ya kamata su yi la’akari da cewa babu wanda zai fi son su idan ba ’yan uwansu Sinawa ba, kuma abun da ya fi masu alheri shi ne dunkulewa da hadewa da ainihin jamhuriyar jama’ar kasar Sin domin ci gaba da samun zaman lafiya.

Babban kuskure ne idan Taiwan da ’yan awarenta suka ci gaba da bayar da kansu ga ’yan kasar waje masu neman fitina. Wannan ba abin da zai tsinana masu sai rikicin da ba wanda ya san yanda zai kare. (Lawal Sale)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Rashin Shugabaci Nagari Ya Jefa Nijeriya Halin Da Take Ciki, In Ji SDP

Next Post

Daga Asabar 8 Zuwa Talata 11 Ga Watan Muharram 1444

Related

Ya Kamata A Kiyaye Nasarorin Da Aka Cimma A Shawarwarin Sin Da Amurka 
Daga Birnin Sin

Ya Kamata A Kiyaye Nasarorin Da Aka Cimma A Shawarwarin Sin Da Amurka 

9 hours ago
Yawan Kadarorin Kamfanoni Mallakar Gwamnatin Sin Ya Wuce Yuan Triliyan 90 a Lokacin Shirin Raya Kasa Na 14 Na Shekaru 5 
Daga Birnin Sin

Yawan Kadarorin Kamfanoni Mallakar Gwamnatin Sin Ya Wuce Yuan Triliyan 90 a Lokacin Shirin Raya Kasa Na 14 Na Shekaru 5 

10 hours ago
Yakin Haraji Da Cinikayya Ba Zai Gurgunta Fifikon Da Sin Ke Da Shi A Fannin Raya Masana’antun Sarrafa Hajoji Da Kasar Ta Gina A Tsawon Lokaci Ba
Daga Birnin Sin

Yakin Haraji Da Cinikayya Ba Zai Gurgunta Fifikon Da Sin Ke Da Shi A Fannin Raya Masana’antun Sarrafa Hajoji Da Kasar Ta Gina A Tsawon Lokaci Ba

11 hours ago
Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Ta CGTN: Baje Kolin Sin Da ASEAN Ya Fadada Matsayar Bai Daya Ta Cudanyar Sassa Daban Daban
Daga Birnin Sin

Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Ta CGTN: Baje Kolin Sin Da ASEAN Ya Fadada Matsayar Bai Daya Ta Cudanyar Sassa Daban Daban

12 hours ago
An Bude Dandalin Tattauna Batutuwan Tsaro Na Xiangshan Karo Na 12 A Beijing 
Daga Birnin Sin

An Bude Dandalin Tattauna Batutuwan Tsaro Na Xiangshan Karo Na 12 A Beijing 

13 hours ago
Har Kullum Burin Sin Shi Ne Wanzar Da Daidaito Da Cimma Moriya Tare Da Amurka
Daga Birnin Sin

Har Kullum Burin Sin Shi Ne Wanzar Da Daidaito Da Cimma Moriya Tare Da Amurka

15 hours ago
Next Post
Gwamnatin Tarayya Ta Ware Biliyan 2.6 Domin Tsaron Abuja

Daga Asabar 8 Zuwa Talata 11 Ga Watan Muharram 1444

LABARAI MASU NASABA

’Yansanda Sun Kama Mutane 9 Kan Yin Ƙaryar Sace Su A Jihar Neja

’Yansanda Sun Kama Mutane 9 Kan Yin Ƙaryar Sace Su A Jihar Neja

September 18, 2025
Sojoji Sun Kama Ƙasurgumin Ɗan Bindiga, Sun Kashe Shugaban IPOB

Sojoji Sun Cafke Babban Kwamandan IPOB

September 18, 2025
Ya Kamata A Kiyaye Nasarorin Da Aka Cimma A Shawarwarin Sin Da Amurka 

Ya Kamata A Kiyaye Nasarorin Da Aka Cimma A Shawarwarin Sin Da Amurka 

September 17, 2025
Yawan Kadarorin Kamfanoni Mallakar Gwamnatin Sin Ya Wuce Yuan Triliyan 90 a Lokacin Shirin Raya Kasa Na 14 Na Shekaru 5 

Yawan Kadarorin Kamfanoni Mallakar Gwamnatin Sin Ya Wuce Yuan Triliyan 90 a Lokacin Shirin Raya Kasa Na 14 Na Shekaru 5 

September 17, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Dawo Da Karatun Tarihi A Makarantu

Gwamnatin Tarayya Ta Dawo Da Karatun Tarihi A Makarantu

September 17, 2025
Yakin Haraji Da Cinikayya Ba Zai Gurgunta Fifikon Da Sin Ke Da Shi A Fannin Raya Masana’antun Sarrafa Hajoji Da Kasar Ta Gina A Tsawon Lokaci Ba

Yakin Haraji Da Cinikayya Ba Zai Gurgunta Fifikon Da Sin Ke Da Shi A Fannin Raya Masana’antun Sarrafa Hajoji Da Kasar Ta Gina A Tsawon Lokaci Ba

September 17, 2025
Manyan Ma’aikatan FIRS 4 Sun Rasu Sakamakon Gobarar Da Ta Tashi A Ginin Afriland A Legas 

Manyan Ma’aikatan FIRS 4 Sun Rasu Sakamakon Gobarar Da Ta Tashi A Ginin Afriland A Legas 

September 17, 2025
Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Ta CGTN: Baje Kolin Sin Da ASEAN Ya Fadada Matsayar Bai Daya Ta Cudanyar Sassa Daban Daban

Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Ta CGTN: Baje Kolin Sin Da ASEAN Ya Fadada Matsayar Bai Daya Ta Cudanyar Sassa Daban Daban

September 17, 2025
Al’ajabi: Yadda Aka Shirya Bikin Haihuwar ‘Ya’yan Awaki Biyar A Garin Dakasoye

Al’ajabi: Yadda Aka Shirya Bikin Haihuwar ‘Ya’yan Awaki Biyar A Garin Dakasoye

September 17, 2025
An Bude Dandalin Tattauna Batutuwan Tsaro Na Xiangshan Karo Na 12 A Beijing 

An Bude Dandalin Tattauna Batutuwan Tsaro Na Xiangshan Karo Na 12 A Beijing 

September 17, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.