Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Ruben Amorim ya ce fatansa shi ne yadda za a kare kakar wasa ta bana kuma su ci gaba da zama a Premier League saboda a halin yanzu idan aka ci gaba da tafiya a haka kungiyar za ta iya fadawa zuwa ajin gajiyayyu idan har sakamakon wasa bai canja ba domin kungiyar tana da wasanni masu wahala a gabanta a yanzu
A ranar Lahadin da ta gabata ne Manchester United ta yi rashin nasara 1-0 a gidan Tottenham a wasan mako na 25 a Premier League, karo na 12 da aka doke kungiyar a bana kuma wasanni takwas kawai kungiya ta ci da canjaras biyar da rashin nasara 12 kuma wannan shi ne kwazo mafi muni tun kakar wasa ta shekarar 1973 zuwa 1913 da ta yi rashin nasara 13 daga nan ta fadi daga gasar.
- Ko Mbappe Zai Lashe Kofin Zakarun Turai Da Ballon d’Or A Real Madrid?
- Ba Zan Yi Ƙasa A Gwiwa Ba Wajen Ceto Manchester City Ba – Guardiola
Saura gurbi biyu ya rage mata ta shiga cikin ‘yan ukun karshe a babbar gasar firimiya ta Ingila ta kakar nan. Sannan Manchester United ta buga karawar ba tare da Ahmad Dialo ba, wanda ke taka rawar gani a kungiyar, wanda aka ce zai yi jinya mai tsawo sanann kungiyar ta fara wasa da Tottenham na ranar Lahadi ba tare da fitattun ‘yan wasa ba, inda Kobbie Mainoo da Manuel Ugarte ke jinya.
Haka kuma masu zaman benci matasa ne guda takwas masu shekara 19 ko kasa da haka da ba su kware ba a buga gasar Premier League. Wasu ‘yan wasan da ba su buga wa United wasan ba sun hada da Christian Eriksen da Leny Yoro da kuma Toby Collyer.
Wasa uku da ke gaban United:
Premier League ranar Asabar 22 ga watan Fabrairu Eberton da Man United
Premier League ranar Laraba 26 ga watan Fabrairu Man United da Ipswich
English FA Cup ranar Lahadi 2 ga watan Maris Man United da Fulham.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp