Rahotonni na cewa, Seymour Hersh, sanannen dan jarida na Amurka, ya wallafa wani sharhi, wanda ya yi bayani dalla dalla tare da ittifakin cewa, jami’an sassan tattara bayanan sirri na Amurka da na sojin kasar ne ke da alhakin lalata babban bututun dake jigilar iskar gas daga kasar Rasha zuwa kasashen Turai, a watan Satumban bara.
Da take amsa tambayar da aka yi mata dangane da wannan batu yayin taron manema labarai na yau Juma’a, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Mao Ning, ta ce akwai bukatar Amurka ta yi wa duniya gamsasshen bayani game da batun.
Ta kara da cewa, butun na da matukar muhimmanci ga kasa da kasa, kuma fashewarsa ya yi mummunan tasiri kan kasuwar makamashi ta duniya da muhallin halittu. Ta kara da cewa, idan har binciken Seymour Hersh gaskiya ne, to abun da Amurka ta yi, abu ne da ba za a lamunta ba kuma dole ta dauki alhakinsa. Tana mai cewa, ya kamata Amurkar ta yi wa duniya bayani.(Faeza Mustapha)