Babban manajan kamfanin Nalado, Injiniya Ma’aruf Isyaku ya bukaci gwamnatoci da su rika amfani da kamfanonin cikin gida wajen aiwatar da ayyukansu wanda hakan zai taimaka wajen kara bunkasa ci gaba a kasa.
Injiniya Isyaku ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron cikar shekara 50 da kafuwar kungiyar injiyoyi ta kasa reshen Jihar Kaduna.
- Daukaka Karar Shari’o’in Zabe: Wasu Hukunce-hukunce Sun Yi Ba-zata
- Bankin TAJ Ya Sake Lashe Kyautar Gwarzon Bankin Musulunci Na Bana
Manajan ya kara da cewa gwamnati tana bukatar kwararrun injiniyoyi domin aiwatar da ayyukan ta. Ya ce bai wa injiniyoyi wanda suke da kwarewa yana matukar taimakawa.
Injiniya Isyaku ya ce akwai bukatar gwamnati ta rinka aiki kafada da kafada da kungiyar injiniyoyi, wanda hakan zai nuna cewa injiniyoyi suna da rawar takawa wajen ciyar da kasa gaba.
Ya bayyana murnasa da cikar kungiyar injiniyoyi ta Jihar Kaduna shekara 50 da kafuwa, wanda hakan ke nuna cewa injiniyoyi a Jihar Kaduna suna da karfi.