• English
  • Business News
Sunday, October 5, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Akwai Bukatar Manyan Jaruman Da Suka Yi Kudi Su Taimaki Na Baya -Barau Dadin Kowa

by Rabilu Sanusi Bena
3 months ago
in Nishadi
0
Akwai Bukatar Manyan Jaruman Da Suka Yi Kudi Su Taimaki Na Baya -Barau Dadin Kowa
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Shafin Rumbun Nishadi, shafi ne da ya saba zakulo muku fitattun jaruman fina-finan Hausa, manya da kanana da ke cikin masana’antar Kannywood, mawaka ma ba a bar su a baya ba cikin wannan shafi.

A yau shafin namu, ya yi tozali ne da daya daga cikin fitattun Jaruman fina-finan hausa da ke masana’antar Kannywood, wato Dauda Sani Dan’asabe, wanda aka fi sani da Malam Barau Dadin Kowa, Jarumin da ya shafe tsawon shekaru da dama a masana’antar, ya bayyana wa masu karatu babban dalilinsa na fara fitowa cikin masana’antar ta Kannywood, ya kuma yi batutuwa masu yawan gaske; dangane da abin da ya shafi rayuwarsa da kuma sana’arsa hadi da irin gwagwarmayar da ya sha a cikin masana’antar.

  • Rashin Ganin Shugabannin APC Yayin Ziyarar Shettima A Kano Ya Haifar Da Zazzafar Muhawara
  • Matatun Man Fetur Na Nijeriya Ba Za Su Ci Gaba Da Aiki Yadda Ya Kamata Ba – Dangote

Ga dai yadda tattaunawar tasa ta kasance tare da wakiliyarmu ta LEADERSHIP, Rabi’at Sidi Bala kamar haka:

Masu karatu za su so jin cikakken sunanka da kuma sunan da aka fi sanin ka da shi.

Sunana Dauda Sani Dan’asabe Adakawa Kano, wanda aka fi sani da Malam Barau Hedimasta Dadin-kowa.

Labarai Masu Nasaba

An Nada Adamar Kamaye Sarautar Jakadiya A Kasar Ghana

Daga Kallon Fina-finan Indiya Na Samu Sha’awar Fadawa Kannywood – Kamalu Mijinyawa

 

Ko za ka iya fada wa masu karatu dan takaitaccen tarihinka?

An haife ni a Unguwar Adakawa cikin birnin Kano, na yi makarantar firamare a Adakawa, daga nan kuma na tafi zuwa makarantar sakandire (Gwammaja One), bayan na sauke Alkur’ani, daga baya na tafi sai na wuce zuwa ‘School of Health Technology’ ta Kano. Bayan nan, sai kuma na tsunduma harkokin kasuwanci da siyasa, kazalika ina da mata biyu da kuma ‘ya’ya goma a halin yanzu.

 

Kamar wane irin kasuwanci kake yi?

Ina harkar takalma ‘yan Kofar Wambai, wadda ita ce sana’ar dana fara koya, sannan kuma ita ce sana’ar da dangina suke yi.

 

Me ya ja hankalinka har ka tsunduma cikin masana’antar Kannywood?

Tun ina yaro na fara was an Dirama, daga makarantar firamare har zuwa sakandire, muna da ‘Drama club’ kafin zuwan kannywood.

 

Idan na fahimce ka, ba a shirin Dadin Kowa ka fara fitowa ba, ka fara ne daga wasan tun daga was an Dabe?

Tun kafin Dadin Kowa, an saba gani na a fina-finan Kannywood, na fara yin shuhura ne a fim din Mugun Iri, na Musa Mai Sana’a.

 

Daga wancen lokacin zuwa yanzu, ka yi kamar shekara nawa da fara wannan harka ta fim?

Fina-finan kannywood, na dauki kamar tsawon shekara goma sha biyar, amma na Dirama, na fara tun a shekarar 1998.

 

Yaya gwagwarmayar farawar ta kasance a wancan lokacin?

Dama kowa ya san dan ‘Drama Club’ ne ni, domin kuwa muna tare da su Tahir Fagge.

 

Yaya batun kalubale, musamman kai da taso a cikin gari, ka fuskanci tsangwama ko wani abu makancin haka daga iyaye, ‘yan’uwa sauran al’ummar unguwa?

Babu wani kalubale, kasancewar yaro ne mai biyayya da girmama na gaba, kuma iyaye suna kaunar ganin ci gaban duk abin da na dauko mai amfani da bai saba wa shari’a ba.

 

Ya farkon fara saka maka Kyamara ya kasance?

Ko kadan ban samu matsala wajen dora Kyamara ba, sakamakon na saba da ita, domin tun wajen shekarun 1984 ina cikin yara ‘yan rawar Bungalo, sannan kuma ina cikin wadanda ake nunawa a Talabijin.

 

Ko za ka iya bambanta wa masu karatu tsakanin wasan Dabe da na Kannywood?

Gaskiya bambancin shi ne, wasan ‘Drama club’, rukunin mutane ne kawai na masu ra’ayin shirya wasannin gargajiyya a fili ko dandali, wanda aka fi sani da wasan Dabe. Hanyar shiga kuma ita ce, kawai yawan zuwa wajen wasan da kuma yin abin da ake so ka yi.

 

A wasannin Dabe, ana tsara muku yadda za ku yi wasan ne kafin lokacin, ko kuwa yaya abin yake?

A wajen ake shirya wasannin, sannan kuma a yi bitar wasan, daga nan kawai sai kan Dandamali, wato ‘stage’, har ma wasu sukan ce ‘Stage Drama’.

 

Su waye abokan sana’arka wadanda ku ka yi wasan Dabe tare a wancen lokacin?

Abokan ‘stage drama’ na su ne; Tahir Fagge, Iyantama, Baba Labaran, akwai kuma irin su Aminu Boss da dai sauransu.

 

Yaya aka yi ka tsinci kanka cikin shirin Dadin Kowa?

To maganar Dadin Kowa, ‘audition’ aka yi na shiga, kuma ban samu nasara ba, na yi hakuri aka kuma sanya wani ‘audition’ din, bayan wani lokaci na kuma zuwa, a wannan karon sai na samu nasarar shiga.

 

A shirin Dadin Kowa, wane waje ka fi so, wane waje ne idan ka tuna yake ba ka dariya, sannan wane waje ne kuma ya fi bata maka rai?

A shirin Dadin Kowa wajen da ya fi ba ni dariya shi ne, lokacin da ina Hidimasta’, inda ‘yan kwamitin P.T.A suka taru za su cire ni daga mukamin, ni kuma na raba kansu na bai wa wasu shugabancin suka koma rigima a junansu. Sai kuma wajen da na kwashe shinkafar ‘yan makarantar na sayo gero, maimakon a rika dafa shinkafar aka koma dama Koko, yara suka rika sha suna barci a makarantar, nan ma ya ba ni dariya. Wajen da ya fi bata min rai kuma shi ne, lokacin da na sayar da gidan marayu na zuba kudin a caca aka cinye, wanda dalilin haka yasa na gudu daga garin Dadin Kowa.

 

Wane irin kalubale ka taba fuskanta, wanda ba za ka taba iya mantawa da shi ba, tun daga kan wasan Dabe, har kawo yanzu da ka ke cikin masana’antar kannywood?

Akwai kalubale da yawa, amma daya daga ciki shi ne; lokacin da na karbi aikin wani Darakta, aka sanya ranar aikin, amma na tashi da rasuwar kakana, bayan an yi masa wanka da ni, sai na tafi wannan aikin ba tare da na je jana’izarsa ba.

 

Wane irin nasarori ka samu game da fim?

Na samu nasarori masu yawa.

 

Ko za ka iya tuna yawan fina-finan da ka fito ciki?

Gaskiya akwai fina-finai da dama, kamar irin su; Ruwan Dare, Rariya, Garbati, Hannu da Hannu, Dangin Miji, Namijin Kishi, Sarah, ‘Yan Bodin da sauransu. Akalla za su kai kusan 80, wasu suna rubuce.

 

A finafinan da ka fito a ciki, wanne ka fi so; kuma me ya sa, sannan akwai wanda ka taba da-ka-sanin fitowa ciki?

Gaba-daya a fina-finan da na yi, na fi son Dadin Kowa, saboda shi ne ya fito da ni daga karamin jarumi zuwa babba.

 

Wace rawa ka fi yawan takawa a fina-finan da kake fitowa a ciki?

Na fi taka rawar mahaifi mai zafin gaske.

 

Da wane jarumi ko jaruma ka fi jin dadin yin aiki, kuma me ya sa?

Jarumar da na fi jin dadin aiki da ita ita ce, Zuwaira Abdulsalam, saboda ta san yadda za ta sanya ni na yi fushi ko kuma ta sauko da ni idan na yi fushin.

 

Ko akwai wata jaruma da ta taba yunkurin ganin ka aure ta a masana’antar?

Babu wata da muka taba ko soyayya, ballantana maganar aure.

 

Ko akwai jaruman da kake sa ran yin fim da su, wadanda ba ka taba yi da su a baya ba?

Ai babu wani jarumi da ya shahara kowaye da ban yi fina-finai da shi ba.

 

Wane ne babban abokinka a cikin masana’antar Kannywood?

Babban abokina a Kannywood shi ne; Hamisu Lamido Iyantama.

 

Bayan taka rawa da kake yi a matsayin jarumi ko akwai wata rawa da kake takawa a masana’antar?

Iya Jarumi ne n, ban taba shirya nawa fim din ba, kuma ba ni da niyya, sai dai nan gaba ta Allah ce.

 

Yaya kake hada aikinka na fim da kuma sana’arka ta takalmi?

Hada harkokina da na harkar fim ba matsala, domin kafin ranar aikin za a sanar da kai, saboda haka sai ka saita harkar ka da kuma ‘location’ din da za ka je.

 

Idan yaronka na sha’awar harkar fim, za ka ba shi dama ya yi?

Hahh..! ai ko waye cikin yarana yake da sha’awar yin fim, zan goyi bayansa har da gudunmawa.

 

Yaya mu’amularka sauran mutane, musamman wadanda zama ya hada ka da su?

Gaskiya wajen mutanen gari, babu wata matsala tsakanina da su, illa soyayya da son barka.

 

Mene ne burinka na gaba game da fim?

Burina na ci gaba, ganin masanaantar ta dawo da darajarta da hada-hadar sayar da aikin da masu ‘producing’ suka kashe kudi a kai.

 

Idan ka zama shugaba a masana’antar Kannywood, wane irin ci gaba za ka kawo wa masana’antar?

Da za a ce zan zama shugaba, zan yi kokari wajen kawo hadin kan manyan jarumai na masanaantar, sannan kuma zan bayar da shawara kan yadda za a yi hada-hadar kasuwar sayar da fina-finan, domin babbar matsalar harkar sayar da aikin, musamman kananan masu shirya fim din. Babban abin da ya kamata a gyara shi ne, kula da jarumai; domin har yanzu wasu masu biyan aikin ba su fahimci abubuwan sun canja ba.

 

Kenan kana nufin, akwai bukatar karin kudi ga su jaruman, kasancewar komai ya yi tsada a halin yanzu ko yaya kake nufi?

Kwarai kuwa, akwai bukatar kara kulawa da jarumai ta kowace hanya, musamman kasancewar mafi yawan jarumai ba masu karfi ba ne, kuma manyan jaruman da suka yi kudi su taimaki na baya.

 

Yaya kake kallon yadda fina-finai yanzu suka koma masu dogon zango, madadin yadda ake yi a baya na takaitaccen lokaci, shin hakan ci gaba ne ko kuwa ci baya ne a harkar?

Gaskiya fina-finan yanzu masu dogon zango ci gaba ne sosai, kuma da yawansu ina ciki.

 

Kana da ubangida a masana’antar Kannywood?

Gaskiya ba ni da ubangida kai tsaye, amma akwai wadanda suka taimake ni kwarai da gaske.

 

Wane kira kake da shi ga masoyanka, har ma da sauran masu kallon fina-finanka?

Kirana ga masoya na shi ne, duk lokacin da suka ga na yi wani abu wanda ba haka suke so ba, to su yi min uzuri; ita harkar fim ba ka umarni ake yi, ba kai ne kake yin abin da kake so ba, akwai mai bayar da umarni.

 

Ko kana da wadanda za ka gaisar?

Ina gaida Sadik Sani Sadik, Isa feroz Khan, Darakta Yaseen Auwal, Musa Mai Sana’a, Sarari classikue da dukkanin sauran abokan aiki.

 

Muna godiya da ba mu lokacinka da ka yi.

Ni ma na gode.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: BarauDadin Kowa
ShareTweetSendShare
Previous Post

Wang Yi Ya Yi Karin Haske Game Da Taron Ministocin Harkokin Wajen Sin Da Amurka 

Next Post

Shugaban Guinea Bissau Ya Bayyana Sin A Matsayin Abokiyar Hulda Ta Hakika

Related

An Nada Adamar Kamaye Sarautar Jakadiya A Kasar Ghana
Nishadi

An Nada Adamar Kamaye Sarautar Jakadiya A Kasar Ghana

10 hours ago
Daga Kallon Fina-finan Indiya Na Samu Sha’awar Fadawa Kannywood – Kamalu Mijinyawa
Nishadi

Daga Kallon Fina-finan Indiya Na Samu Sha’awar Fadawa Kannywood – Kamalu Mijinyawa

7 days ago
Jaruman
Nishadi

Babu Wanda Ya Jawo Ra’ayina  Zuwa Masana’antar Kannywood —Umar Hassan (2)

2 weeks ago
Ina Fatan Watsi Da Harkar Fim Nan Gaba —Umar Hassan
Nishadi

Ina Fatan Watsi Da Harkar Fim Nan Gaba —Umar Hassan

3 weeks ago
Ban Taɓa Nadamar Shiga Fim Ba – Kabiru Nakwango
Nishadi

Ban Taɓa Nadamar Shiga Fim Ba – Kabiru Nakwango

3 weeks ago
Duk Wanda Ya Girme Ni Ubangidana Ne A Harkar Fim – Hauwa Garba (2)
Nishadi

Duk Wanda Ya Girme Ni Ubangidana Ne A Harkar Fim – Hauwa Garba (2)

4 weeks ago
Next Post
Shugaban Guinea Bissau Ya Bayyana Sin A Matsayin Abokiyar Hulda Ta Hakika

Shugaban Guinea Bissau Ya Bayyana Sin A Matsayin Abokiyar Hulda Ta Hakika

LABARAI MASU NASABA

Me Yarjejeniyar Kawo Karshen Yakin Gaza Da Amurka Ta Tsara Ta Kunsa?

Me Yarjejeniyar Kawo Karshen Yakin Gaza Da Amurka Ta Tsara Ta Kunsa?

October 4, 2025
Firaministan Pakistan: Shugaba Xi Jinping Shugaba Ne Mai Hangen Nesa

Firaministan Pakistan: Shugaba Xi Jinping Shugaba Ne Mai Hangen Nesa

October 4, 2025
Kokarin Da ‘Yan Wasan Nijeriya Suka Yi Wajen Lashe Kyautar Ballon d’Or

Kokarin Da ‘Yan Wasan Nijeriya Suka Yi Wajen Lashe Kyautar Ballon d’Or

October 4, 2025
Jonathan Ya Ƙaryata Batun Danganta Buhari Da Boko Haram

Jonathan Ya Ƙaryata Batun Danganta Buhari Da Boko Haram

October 4, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Kasa Da Kasa Su Ki Amincewa Da Takunkumin Bangare Daya

Sin Ta Yi Kira Ga Kasa Da Kasa Su Ki Amincewa Da Takunkumin Bangare Daya

October 4, 2025
Kasar Sin Ta Soki Matakan Harajin Amurka “Na Ramuwa” A WTO

Kasar Sin Ta Soki Matakan Harajin Amurka “Na Ramuwa” A WTO

October 4, 2025
Jami’ar Nsukka Ta Ce Shaidar Digirin Ministan Fasaha, Uche Nnaji, Ta Bogi Ce

Jami’ar Nsukka Ta Ce Shaidar Digirin Ministan Fasaha, Uche Nnaji, Ta Bogi Ce

October 4, 2025
Jami’in MDD: Shawarar GGI Za Ta Jagoranci Duniya Zuwa Samun Kyakkyawar Makoma Mai Cike Da Adalci

Jami’in MDD: Shawarar GGI Za Ta Jagoranci Duniya Zuwa Samun Kyakkyawar Makoma Mai Cike Da Adalci

October 4, 2025
Nijeriya Ta Samu Kwarin Gwiwar Zuwa Kofin Duniya

Nijeriya Ta Samu Kwarin Gwiwar Zuwa Kofin Duniya

October 4, 2025
Bayan Janyewar Sojojin Kamaru, Boko Haram Sun Dawo Kashe-Kashe A Borno

Bayan Janyewar Sojojin Kamaru, Boko Haram Sun Dawo Kashe-Kashe A Borno

October 4, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.