Kocin kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Carlo Ancelotti, ya bayyana cewar akwai bukatar mahukunta da magoya bayan kungiyar su bai wa Kylian Mbappe lokaci da goyon baya domin ya dawo kan ganiyarsa.
Ancelotti, ya bayyana haka ga ‘yan jarida bayan wasan da Real ta yi rashin nasara a hannun Athletico Bilbao a San Mames a daren Laraba.
- Majalisar Wakilai Ta Dakatar Da CBN Daga Sallamar Ma’aikata 1000
- Sin Ta Jaddada Kudurinta Na Kara Inganta Daidaito Da Tsaro A Tekun Guinea
Mbappe, ya barar da bugun daga kai sai mai tsaron raga a wasan wanda ya janyo masa suka daga magoya bayan kungiyar.
Ancelotti, ya ce Mbappe sabon dan wasa ne wanda ya fara buga wasa a wannan kakar, don haka akwai bukatar a ba shi lokaci da goyon baya domin ya ci gaba da taka rawar gani kamar yadda aka san shi.