Ma’aikatar harkokin wajen Sin ta ce kasar na fatan Amurka za ta cika alkawarin da ta yi cewa, ba ta neman sabon yakin cacar baka ko rikici da kasar Sin, kuma za ta hada hannu da Sin din wajen mayar da huldarsu bisa turbar da ta dace.
Kakakin ma’aikatar Mao Ning ce ta bayyana haka a jiya, yayin da take amsa tambaya game da ganawar shugabannin kasashen biyu dake tafe.
- Xi Jinping Ya Tashi Zuwa Kasar Amurka Domin Gudanar Da Taron Shugabannin Kasashen Sin Da Amurka Da Taron APEC Karo Na 30
- Xi Ya Aike Da Wasikar Taya Murna Ga Taron Shekara-shekara Na ’Yan Kasuwan Mashigin Taiwan
Ta ce tuni Sin ta sanar da cewa shugabanta Xi Jinping zai ziyarci Amurka bisa gayyatar da aka yi masa, tana mai cewa, shugabannin biyu za su yi tattaunawa mai zurfi kan muhimman batutuwan da suka shafi kyautata dangantakar kasashensu da ma manyan batutuwan dake da alaka da zaman lafiya da ci gaban duniya.
Ta ce a huldarta da Amurka, kasar Sin ta kasance mai bin ka’idojin mutunta juna da dangantakar moriyar juna da shugabanta ya gabatar. Kuma takara tsakanin kasashe ba ta dace da yanayin da ake ciki ba, haka kuma ba za ta warware matsalolin Amurka ko kalubalen duniya ba.
Da aka tabo batun Taiwan, Mao Ning ta ce wannan batu ne na cikin gidan Sin da al’ummarta ne kadai za su iya warwarewa. Kuma yayin ganawar da suka yi a tsibirin Bali, gwamnatin Amurka ta bayyana karara cewa ba ta goyon bayan ‘yancin kan yankin, don haka ya kamata ta kiyaye tare da bin manufar kasar Sin daya tak a duniya, kana ta yi adawa da ayyukan dake neman ‘yancin kan Taiwan.
Dangane da batun Tekun Kudancin Sin kuwa, kakakin ta ce a shirye Sin take ta warware matsalar tare da kasashe masu ruwa da tsaki ta hanyar tattaunawa da tuntubar juna. Haka kuma a shirye take ta kare cikakken ‘yanci da yankunanta.
Har ila yau, Mao Ning ta bayyana cewa, duniya na sa ido sosai kan rikicin Palasdinu da Isra’ila, kuma har kullum, Sin na goyon bayan adalci, kana tana tuntubar dukkan bangarori, kuma burinta shi ne ganin an dakatar da rikicin tare da kare fararen hula.
Ta ce Sin na fatan Amurka za ta dauki matsayar da ta dace da taka rawar gani wajen ganin an dakatar da bude wuta nan ba da jimawa ba. (Fa’iza Mustapha)