Babban Editan jaridar yanar gizo ta Daily Nigerian,Jaafar Jaafar ya bayyana cewa, “Tun da gwamna bai ba wa na kusa da shi dama ko fuska su ba shi shawara ba, to kuwa lallai haƙƙi ya rataya a kan duk mai kishin Kano ya faɗa masa gaskiya. “
“Mai girma Gwaman Kano, Abba K. Yusuf, sai ka gyara mu’amillarka da mashawartanka da kuma masu riƙe da muƙaman gwamnati.”
- Sheikh Daurawa Ya Sauka Daga Muƙaminsa Na Shugaban Hisbah Kano
- Rikita-rikitar ‘Yar Tiktok Murja Kunya Da Hukumar Hisba A Kano
“Zancen da mu ke ji shi ne kwamishina sai ya yi wata da watanni ya na son ganin gwamna kan abu mai muhimmanci amma ya kasa gani ko magana da gwamna ta waya. Wannan bai kamata ba, domin kuwa hannu ɗaya ba ya ɗaukar jinka.”
“Binkicen da na yi ya nuna cewa Mallam Daurawa ya yi yunƙurin ganin gwamna don tattauna da shi kan matsalar Murja Kunya amma gwamna bai ba shi dama ba. Ya yi yunƙurin yi masa bayani ta waya, nan ma abin ya ci tura.”
“Sukar da gwamna ya yi wa Hukumar Hisba jiya a bainar jama’a kamar mutum ne ya daɓa wa kansa wuka, domin kuwa gwamnatinsa ya zaga. Kuma dole jama’a su ce saboda Hisba ta kama Murja Kunya gwamna ya yi wannan magana, domin kuwa a lokacin da Hisba ta ke kama masu baɗala ta na jefa su a bayan mota gwamna bai ce uffan ba sai bayan an kama wannan yarinya.”
“Duk mai hankali ya san cewa akwai hannun gwamna (ba wani gwamnati, GWAMNA) dumu-dumu a fitar da murja daga gidan yari ba bisa doron doka ba.”
“ ‘Yan watannin baya kamar mu haukace saboda ana yunƙurin kawar da gwamnatinka ba bisa doron doka ba, amma abin takaici kai kuma ka yi wa doka hawan ƙawara saboda wata ballagaza bankaura.” Cewar dan jarida Jaafar Jaafar.