Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) a jihar Kano ta bayyana cewa akwai katin zaɓe na dindindin (PVC) sama da dubu 367,000 da jama’a ba su karɓa ba har yanzu a jihar.
Kwamishinan INEC na Kano, Ambasada Abdu Zango, ya bayyana haka ne yayin da ya karɓi tawagar kwamitin gwamnatin jihar kan rajistar katin zaɓe ƙarƙashin jagorancin kwamishinan yaɗa labarai, Ibrahim Abdullahi Waiya. Ya yabawa matakin kafa kwamitin tare da kira ga mambobinsa da su ƙara ƙaimi wajen wayar da kan jama’a domin su tafi su karɓi katin zaɓensu.
- Tanko Yakasai Ya Nuna Takaici Kan Rashin Samar Da Kamfanin Sarrafa Fata A Kano Kamar Na Legas
- 2027: ‘Yan Siyasa Sun Yi Watsi Da Gargadin INEC, Sun Ci Gaba Da Yakin Neman Zabe
Zango ya ƙara da cewa jihar Kano tana da masu zaɓe sama da miliyan 6 da aka riga aka yi wa rajista, wanda fiye da miliyan 3.6 daga cikinsu ke cikin ƙananan hukumomin birnin Kano.
A nasa jawabin, Waiya ya jinjinawa INEC bisa ci gaba da gudanar da aikin rajista tare da roƙon a ƙara samar da rumfunan zaɓe da cibiyoyin rajista a wuraren da ke da wahalar isa. Ya ce hakan zai sauƙaƙa wa jama’a kuma ya tabbatar da cewa ba a bar wani ɗan ƙasa da ya cancanta ba a baya. Ya ƙara da cewa kwamitin zai ci gaba da amfani da dabaru wajen motsa jama’a domin yin rajista da kuma karɓar katin zaɓensu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp