Ga duk mai bibiyar muhimman harkokin dake gudana a ’yan kwanakin nan, ba zai gaza lura da yadda hankula suka karkata ga ziyarar da shugaban kasar Sin Xi Jinping yake yi a kasar Amurka ba, duba da yadda wannan ziyara ta yi matukar jan hankulan sassan kasa da kasa, inda tuni shugaba Xi ya gana kai tsaye tare da takwaransa na Amurka, kuma mai masaukinsa Joe Biden, a katafaren gidan alfarman nan na Filoli dake birnin San Francisco, ganawar ido da ido da ta kasance ta farko tsakanin shugabannin biyu, tun bayan haduwarsu a tsibirin Bali na Indonesia a shekarar bara.
Bayan tattaunawa tsakanin shugabannin biyu game da muhimman batutuwa, da musayar ra’ayoyi kan abubuwan dake matukar jan hankulan kasashensu, musamman wadanda suka jibanci yadda za a farfado, da kara kyautata dangantakar Sin da Amurka, da ma batutuwan dake shafar zaman lafiya da ci gaban duniya, da dama daga masharhanta na ganin ganawar ta yi armashi.
- Kotun Daukaka Kara Ta Ayyana Zaben Gwamnan Zamfara A Matsayin Bai Kammala Ba
- Sin Da Afirka Na Da Makoma Mai Kyau A Fannin Hadin Gwiwar Aikin Gona
Har ma wasu masu fashin baki na ganin shugabannin kasashen biyu, suna sane da cewa duniya ta zuba ido domin ganin rawar da za su taka a wannan gaba da duniya ke fuskantar manya manyan kalubale a mataki na kasa da kasa da ma na shiyyoyi.
Duniya ta yi imanin cewa, alakar Sin da Amurka tana da muhimmancin koli, kuma kyautatarta zai ingiza ci gaban duniya, don haka ya dace a yi duk mai yiwuwa wajen inganta ta.
Masu fashin baki sun dade da amincewa, cewa idan har Sin da Amurka suka juyawa juna baya, hakan zai haifar da mummunan sakamako ga duniya, baya ga illar da hakan zai yi a gare su, don haka ba hanya ce mai bullewa ba. Kaza lika ba abu ne mai yiwuwa daya daga cikin manyan kasashen biyu ta yi yunkurin sauya dayar ba, kuma rura wutar rikici, ko fito na fito tsakanin su ba zai haifarwa kowa da mai ido ba.
Tabbas, mummunar takara tsakanin manyan kasashe masu fada a ji ba ta dace da muradun wannan zamani ba, kuma hakan ba zai warware tarin kalubale da Sin da Amurka ke fuskanta, da ma matsalolin sauran sassan duniya ba. Don haka fatan dukkanin sassan kasa da kasa a wannan gaba da wadannan shugabanni na manyan kasashen duniya ke tattaunawa, shi ne su kai ga cimma nasarar dinke baraka, su rungumi juna, tare da amincewa cewa nasarorin da suke cimmawa, damammaki ne na bunkasar juna.
Ko shakka babu, muddin kasashen Sin da Amurka sun martaba juna, sun rungumi hadin gwiwar cimma moriya tare cikin lumana, bangarorin biyu za su cimma nasarar shawo kan sabanin dake tsakaninsu, tare da zakulo hanya madaidaiciya ta zaman jituwa mai alfanu. (Saminu Alhassan)