Kotun daukaka kara da ke Abuja ta soke zaben Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), ta bayyana Lawal a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.
- Sin Da Afirka Na Da Makoma Mai Kyau A Fannin Hadin Gwiwar Aikin Gona
- Kasashen Afirka Na Cin Gajiyar Aikin Zamanintar Da Aikin Gona Na Sin
Sai dai jam’iyyar APC, ta kalubalanci nasarar Lawal, wanda ya tsaya takara a karkashin jam’iyyar PDP.
Talla
Kotun sauraren kararrakin zabe ta amince da zaben Lawal, amma APC ta garzaya kotun daukaka kara.
A ranar Alhamis ne wani kwamitin alkalai uku ya soke nasarar Lawal tare da bayar da umarnin sake gudanar da zaben a kananan hukumomi uku.
Kananan hukumomin da abin ya shafa sun hada da Maradun, Birnin Magaji da Bukuyun.
Talla