ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, November 12, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Akwai Makoma Mai Haske Game Da Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

by CMG Hausa
3 years ago
Sin

A baya bayan nan, hukumar lafiya ta duniya WHO ta bayyana raguwar adadin masu harbuwa da cutar COVID-19 a nahiyar Afirka da kaso mai yawa, tun daga tsakiyar watan Afirilun da ya gabata, raguwar da a cewar hukumar ita ce mafi tsawo da aka samu a nahiyar tun bullar wannan annoba kawo yanzu.

Ko shakka babu wannan labari ne mai faranta rai ga duniya baki daya. To sai dai kuma, wani jan aiki dake gaban kasashen nahiyar ta Afirka a yanzu shi ne lalubo hanyoyin shawo kan mummunan tasirin da wannan annoba ta haifar musamman ta fuskar tattalin arzikin Afirka.

  • Sin Tana Adawa Da Dokar Hana Kayayyakin Da Suka Shafi Jihar Xinjiang Shiga Amurka

Hakan ne ma ya sa masharhanta da dama ke ganin ya zama wajibi kasashen Afirka su karfafa hadin gwiwarsu da kasar Sin, karkashin muhimman manufofin hadin kai da sassan biyu suka jima da amincewa da su, wadanda suka hada da manufofin da aka tsara karkashin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka, da ayyukan samar da moriya dake kunshe cikin shawarar nan ta ziri daya da hanya daya da sauran su.

ADVERTISEMENT

A halin da ake ciki, kasar Sin ce babbar abokiyar huldar nahiyar Afirka ta fuskar kasuwanci cikin sama da shekaru 10, kuma kasar da kamfanoninta ke kara zuba jari mai yawan gaske a nahiyar, wanda adadinsa ya karu a watanni 7 na farkon shekarar 2021 zuwa dalar Amurka biliyan 2.07.

A bangaren nahiyar Afirka, masana na cewa, nahiya ce dake da tarin albarkatun kasa, da maadanai masu daraja, da man fetur da iskar gas, da damar samar da makamashi daga hasken rana, da fadin kasar noma mai yalwa, da tarin alumma dake cikin shekarun kwadago.

LABARAI MASU NASABA

Xi Ya Gana Da Sarkin Sifaniya A Birnin Beijing

Sin Ta Yi Kira Da A Inganta Mika Mulki Cikin Kwanciyar Hankali A Sudan Ta Kudu

Sai dai kuma kalubalen rashin masanaantu, da kamfar makamashi, ya zamowa nahiyar kadangaren bakin tulu, ta yadda kasashen nahiyar ba sa samun damar cin gajiyar da ta dace daga albarkatunta. Hakan ya sa kasashen Afirka da dama kasancewa cikin jerin kasashe mafiya fama da talauci a duniya.

Duk da wadannan tarin kalubale, akwai makoma mai haske ga kasashen na Afirka, muddin sun ci gaba da nacewa aiwatar da kudurorin dake kunshe cikin ajandojin wanzar da ci gaban su, tare da babbar manufar nan ta raya hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka ta nan da shekarar 2035, ko China-Africa Cooperation Vision 2035 a Turance, da ma shirin dandalin bunkasa hadin gwiwar Sin da Afirka na Dakar, mai kunshe da tsarin ayyuka da za a aiwatar tsakanin shekarar nan ta 2022 zuwa 2024.

Dukkanin wadannan kudurori ne da ke kunshe cikin babbar manufar nan ta shawarar ziri daya da hanya daya da kasar Sin ta gabatarwa duniya, wadda ko shakka babu, ci gaba da aiwatar da ita zai haifarwa kasashen na Afirka tarin alfanu nan da shekaru masu zuwa. (Saminu Hassan)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Xi Ya Gana Da Sarkin Sifaniya A Birnin Beijing
Daga Birnin Sin

Xi Ya Gana Da Sarkin Sifaniya A Birnin Beijing

November 12, 2025
Sin Ta Yi Kira Da A Inganta Mika Mulki Cikin Kwanciyar Hankali A Sudan Ta Kudu
Daga Birnin Sin

Sin Ta Yi Kira Da A Inganta Mika Mulki Cikin Kwanciyar Hankali A Sudan Ta Kudu

November 12, 2025
Sin: Amurka Ba Ta Sa Lura Ga Kare Hakkin Dan Adam
Daga Birnin Sin

Sin: Amurka Ba Ta Sa Lura Ga Kare Hakkin Dan Adam

November 11, 2025
Next Post
Yadda Wani Lauya Ya Tarwatsa Dakin Shari’a Da Shigar Matsubbata

Yadda Wani Lauya Ya Tarwatsa Dakin Shari'a Da Shigar Matsubbata

LABARAI MASU NASABA

Majalisar Kogi Ta Dakatar Da Shugaban Ƙaramar Hukuma Bisa Zargin Rashin Ɗa’a

Majalisar Jihar Kogi Ta Dakatar Da Shugaban Ƙaramar Hukuma Kan Laifin Rashin Ɗa’a

November 12, 2025
Xi Ya Gana Da Sarkin Sifaniya A Birnin Beijing

Xi Ya Gana Da Sarkin Sifaniya A Birnin Beijing

November 12, 2025
Bikin Baje Koli CIIE, Bikin Zaburar Da Manoman Afirka

Bikin Baje Koli CIIE, Bikin Zaburar Da Manoman Afirka

November 12, 2025
Yadda Jami’an ‘Yansanda Suka Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja, Sun Kwashe Fiye Da Naira Miliyan 20 A Asusunsa

An Kama Direban Gwamnati Da Hannu A Satar Motar Ofishin Mataimakin Gwamnan Kano

November 12, 2025
Sin Ta Yi Kira Da A Inganta Mika Mulki Cikin Kwanciyar Hankali A Sudan Ta Kudu

Sin Ta Yi Kira Da A Inganta Mika Mulki Cikin Kwanciyar Hankali A Sudan Ta Kudu

November 12, 2025
Za Mu Kare Sojojin Da Ke Bakin Aiki — Ministan Tsaro

Za Mu Kare Sojojin Da Ke Bakin Aiki — Ministan Tsaro

November 12, 2025
‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 3 Tare Da Sace Babur A Nasarawa

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 3 Tare Da Sace Babur A Nasarawa

November 12, 2025
‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi Sama Da 200 A Katsina

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi Sama Da 200 A Katsina

November 12, 2025
Injiniya Sagir Ibrahim Ƙoƙi Ya Fice Daga Jam’iyyar NNPP

Injiniya Sagir Ibrahim Ƙoƙi Ya Fice Daga Jam’iyyar NNPP

November 12, 2025
Bayanan Da Muka Samu Sun Nuna An Fara Samun Tsaro A Nijeriya – Hafsan Sojin Ƙasa

Bayanan Da Muka Samu Sun Nuna An Fara Samun Tsaro A Nijeriya – Hafsan Sojin Ƙasa

November 12, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.