Kungiyar Al Ahly ta Masar, ta dauki kofin zakarun Afirka na 12 jimilla, bayan da ta ci Esperence 1-0 a wasan karshe na biyu a Birnin Cairo ranar Asabar bayan da a makon da ya gabata suka tashi ba ci a wasan farko a Tunisia, daga nan aka buga fafatawa ta biyu a Masar, inda Al Ahly ta dauki kofin kakar nan.
Minti hudu da fara wasa Roger Aholou ya ci gida, bayan da El Shahat ya bugo kwallo, Rami Rabia ya sa kai, sai ta bugi Roger ta fada raga kuma Al Ahly ta yi ta kokarin kara kwallo ta biyu a raga ta hannun Wessam Abou Ali da kuma Percy Tau, amma hakan bai yiwu ba.
- Yawan Wutar Lantarki Da Jerin Madatsun Ruwa Dake Sin Suka Samar A Rubu’in Farko Na Bana Ya Zarce Kilowatts Biliyan 52
- Alkiblar Da Nijeriya Ta Dosa Cikin Shekara 25 Na Dimokuradiyyarta
Sai dai kadan ya rage El Shahat ya ci wata kwallo, amma mai tsaron raga, Amanallah Memmiche ya tare amma kungiyar wadda Marcel Koller ke jan ragama ta kammala kakar bana ba tare da an doke ta ba – kamar yadda ta taba wannan bajintar a kakar wasa ta 2005 zuwa 2006 haka kuma mai tsaron raga Mostafa Shobeir ya yi wasa tara a jere kwallo ba ta shiga ragarsa ba.
Haka kuma kungiyar ta kasar Masar ta yi wasanni 22 a gasar zakarun Afirka ba tare da rashin nasara ba, sannan ta lashe Champions League na Afirka karo na biyu a jere, na hudu tana irin wannan bajintar.
Tuni dai Al Ahly da Esperance suka samu tikitin sabuwar gasar Fifa da za ta kunshi kungiyoyi 32 a sabon fasalin Club World Cup a 2025 kuma za a gudanar da wasannin a Amurka a watan Yuni zuwa Yulin badi har da kungiyoyin Wydad Casablanca da kuma Mamelodi Sundowns a cikin wasannin.