Kungiyar kwallon kafa ta Al-Hilal dake Saudi Arabiya, ta zama ta farko da ta kafa tarihin cin wasa da yawa a jere, bayan da ta doke Al-Ittihad 2-0 a gasar cin kofin Champions League na Asia.
Wasa na 28 a jere kenan da kungiyar ta yi nasara jimilla da ba mai wannan tarihin a duniya kuma wadda ke rike da bajintar a baya ita ce wata kungiya a Wales, The New Saints a 2016 wadda ta yi nasarar cin wasa 27 a jere.
- Ana Amfani Da Na’urar Hakar Mai Ta Zamani Da Kamfanin Sin Ya Kera A Uganda
- Uwargidan Shugaban Kasa Ta Bude Makaranta Ga Matan Da Aka Kora AÂ Manyan Makarantu A Bauchi
Al-Hilal, wadda take da fitattun ‘yan wasa ciki har da tsohon dan wasan Fulham, Aleksandar Mitrobic ta ci wasa 28 a jere tun daga 1-1 da Damac ranar 21 ga watan Satumba.
Shima tsohon dan wasan Wolbes, Ruben Nebes na buga wa Al-Hilal wasa har da dan kwallon Brazil, Neymar, wanda ya koma kungiyar daga Paris St-Germain kan kudi fam miliyan 77.6 har da tsarabe-tsarabe.
Koda yake Neymar na jinya tun raunin da ya ji a cikin watan Oktoba kuma har yanzu bai warke ba duk da cewa a kwanakin baya an fara rade radin cewa kungiyar za ta soke kwangilar da suka kulla da dan wasan.
Al-Hilal, wadda tsohon kociyan Benfica da Flamengo, Jorge Jesus ke jan ragama tana ta dayan teburi a babbar gasar Saudi Arabiya ta bana, sannan ta kuma bai wa kungiyar da Cristiano Ronaldo ke buga wasa wato Al-Nassr tazarar maki 12.
Dan wasa Mitrobic ya ci kwallo 26 daga 81 da Al-Hilal ta zura a raga a wasa 28 da ta yi nasara a jere kuma ta lashe wasa 16 a lik da uku a wasannin cikin gida da kuma tara a Champions League na Asia.
Nasarar da Al-Hilal ta yi ranar Talata ya sa ta ci kwallo 4-0 gida da waje ta kuma kai dab da karshe a gasar zakarun Turai ta Asia ya yin da tuni aka doke kungiyar Al-Nassr da Cristiano Ronaldo yake bugawa wasa.