(Na taba gabatar da wannan kasida a jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo ta ranar litinin 25 ga watan Janairun shekarar 1999).
Ma’anar Tashe
Kalmar TASHE ana kyautata zaton ta yo asali ne daga Kalmar TASHI ko TASA. Wato kamar ka tashi mutum daga barci ko daga zaune ko kishingide. wasan Tashe kuwa na nufin ta da/tayar da mutum cikin raha da nishadi da kayatarwa.
Tashe wasa ne da ya yi suna kuma ya shahara a kasar Hausa. Ana yinsa ne a lokacin da wata Azumi ya kai goma. Wasa ne da bai bar kowa ba domin kuwa ba babba babu yaro, ba mace babu namiji kowa yakan yi irin nasa daidai gwargwado.
Tarihin Tashe
Wasu sun ce Tashe ya shigo kasar Hausa ne bayan zuwan addinin musulunci a karni na goma sha daya idan aka lura da fasalinsa da kyau. Akan yi Tashe da daddare a wadansu wuraren ma har da rana ana yi ko da safe. Akwai Tashe iri-iri a kalla iri dari. Wadansu masu ban dariya, wadansu su ilimantar tare da nishadantarwa. Wasu kuwa cike da abubuwan tausayi da ban al’ajabi ko tarihi. Wadansu maza zar ke yinsu, wadansu kuwa ‘yan mata. A wasu Tashen akan samu haduwar ‘yan maza da ‘yan mata, kuma kamar yadda yara ke wasan Tashe haka nan manya ma ke yi.
Misalan Tashe
Misalin wasan Tashe na ‘yan maza zar shi ne Tashen Macukule, inda shi jagoran Tashen zai sanya wata irin fuska ko ya shafe fuskarsa da bula ko toka, sauran ‘yan wasan kuma suna biye da shi yana sa waka suna amsa masa kamar haka:
Jagora: Kan kare da dadi.
‘Yan amshi: Macukule
Jagora: Majina Kitse ce
‘Yan amshi: Macukule
Jagora: Kan agwagwa taushe
‘Yan amshi: Macukule
Wannan Tashe na Macukule bayan kasancewarsa na maza zar ne, har ila yau yana taimaka wa mutum sanin irin wasan (barkwanci) da ke tsakanin Hausa da Gwari/Gbagi, domin kuwa irin wannan wasa ko yi wa juna barkwanci, ba sabon abu ba ne a tsakanin Hausa da Fulani, Fulani da Barebari, Hausawa da Inyamurai, Kanawa da Zage-zagi da dai sauran kabilu da aka taba samun wata dangantaka a tsakaninsu da Hausawa.
Sauran Tashen da maza kadai ke yi sun hada da:
- Ka yi rawa kai malam ka yi rawa
- Jatau mai magani
- Mai kiriniya
- Tsoho da gemu da dai sauransu.
Na ‘yan mata zalla kuwa sun hada da:-
- Mai ciki
- Iya duba cikina
- Hajiyar kauye
- Mairama ga Daudu
‘Yan Tashe kan bi gida-gida, ko kasuwanni ko kauyuka da tituna ko birane domin yin Tashen, kuma duk inda suka yi Tashen akan yi masu dan abin hasafi. Akan ba su gero ko dawa ko kudI, in kuma kasuwa suka shiga su samo kayan miya da sauran abubuwa da ke wannan kasuwa.
Muhimmancin Tashe
Tashe yana da muhimmanci kwarai da gaske da in muka ce za mu tsaya lissafa muhimmancinsa sai mun kusan shekara ba mu kamala ba. Baya ga irin nishadantar da jama’a da wasan Tashe ke yi, har ila yau Tashe tamkar wata taska ce da ke makare da al’adar Hausawa domin kuwa da zaran lokacin ya kewayo sai ya sa tsofaffi sun tuna lokacin da suke yara. In ba yanzu da dinbin bakin abubuwa suka samu gindin zama a cikin Tashen ba, in ka kira Tashe da sunan MADUBIN HOTON ADABIN HAUSA ba karya ka yi ba.
Har ila yau wasan Tashe na taimaka wa yaro wajen kara fahimtar al’adarsa da al’umarsa wadanda za su yi tasiri wajen tarbiyyantar da shi a matsayin yara manyan gobe, da kuma kara masa basirar yadda zai yi amfani su ta hanyoyin da suka dace.
Hasali ma Tashe na taimaka wa sauran al’uma da ke makwabtaka da Hausawa kamar su Inyamurai da Yarbawa da sauran kabilu su fahimci Hausawa da zamantakewarsu, da addininsu da siyasarsu har su yaba.
A zamanin da, Tashe yana daya daga cikin kwararan hanyoyi tattaro yara, da dan manomi da na masaki, da na maharbi da na mahauci da sauransu zuwa wuri guda, su shirya wasannin Tashe iri-iri har na tsawon kwana ashirin. Har in suna yawon Tashen akan gamu da wasu ‘yan Tashen da kan ce ‘Kura ta ci kura’ Ku kuma ku mayar da martini ku ce ‘Ta ci in ta samu’
Kuma ana amfani da tashe wajen karfafa wa al’umar Musulmi kwarin gwiwar kara dukufa ga bauta wa Ubangiji kamar yadda yake a cikin tashen nan da ake cewa:-
Jagora: A sha ruwa-ruwa a sha ruwa ai sallah,
‘Yan amshi: A sha ruwa
Jagora: masu gidan nan barci kuke ko sallah,
‘Yanamshi: A sha ruwa
Jagora :In barci ne ku tashi domin Allah,
‘Yan amshi: A sha ruwa
Jagora: In sallah ce ku yi ta domin Allah.
Matsalolin Tashe a Yau
To abin ban takaici shi ne duk da wadannan dinbin muhimmancin da Tashe yake da su, yana ta kara samun fuskantar kisan gilla daga ko ta wane bangare. Muhimmi daga cikin irin matsalolin da suka dabaibaye Tashe shi ne watsi da Hausawa suka yi da al’adar ta Tashe, ballantana har su yi tunanin habaka shi.
Kusan babu wani kokarid a manyan malaman Hausa da ke tsibe a manyan makarantunmu na ilimi. Su kuma yara a yanzu sai kwallon kafa da kallon fina-finai da sauran karance-karance da suka saba wa dabi’arsu.
Bugu da kari ga satar yara da ake ta fama da ita a yanzu da ya sa kowa idan yamma ta yi sai ya garkame ‘ya’yansa a gida ko leke babu.
Sannan yanayi kan canza domin a wasu lokutan za ka ga Tashe ya fado a lokaci na hunturu ko damina da yaran ko dai dari ya hana su fita, ko in sun fita ruwan sama ya musu duka. Ko sun nace sun yi tashen, gidajen da za su shiga yin Tashen za su tarar kowa ya kulle kofarsa babu kowa a tsakar gida.
Su kuma gidajen rediyon da ke Arewacin kasarnan musamman gidan Rediyon Tarayya na Kaduna suna kokarin sanya wasannin Tashen da watan Azumi, sai dai su ma sun rage himma da lokaci saboda kudi da aka dage ana nema, ake ta fafutukar neman wadanda za su dau nauyin sanya Tashen. Wata kila shi ya sanya gidan Rediyon Tarayya na Kaduna ya rage lokutan sanya Tashen. In kuwa haka ne, to wannan babbar kalubale ce ga sassan nazarin harshen Hausa da muke das u a jami’o’inmu. In wani bai iya daukar wannan nauyi, su hakkinsu ne su dauka kamar yadda sassan binciken aikin noma na jami’o’I ke yi a su talabijin da rediyo.
Wani abin kuma da ke barazana ga Tashe shi ne tabarbarewar da tattalin arzikin kasarnan ya yi da jefaal’umarta cikin halin kaka-ni-kayi komai ya tsauwala gas hi ba kudi. Gidaje da yawa sai ka tarar an yi kwana da kwanaki ba a dora sanwa ba. To ina ga wadanda suka zo Tashe? A da bayan an kare kwanakin Tashe sai ka tarar yara sun tara hatsi kusan buhu ko buhunhuna. Amma a yanzu ko mudu ba sa hadawa. Haka zalika za su kare bas u sami ko kwabo ba, wasu wuraren ma idan sun je ko dai a kore su, ko a mayar da su marasa aikin yi, ko kauyawa.
Mafita
Ina mafita? Tunda mun san irin matsalolin da ke addabar Tashe, ya zama wajibi akan duk wanda ya san yana da hakki a kai musamman Hausawa da sauran cibiyoyin ilmi da ke da nasaba da harshen Hausa da sauran kungiyoyin Hausa, su mike tsaye su yi wani abu akai, in ba haka ba su wayi gari wata rana su tarar Tashe ya sheka lahira sai labara.
IS’HAK IDRIS GUIBI, Kaduna, ana iya samun sa ta: