Wani abu mai kama da wasan kwaikwayo da ya faru a Kano ranar Alhamis, inda wani Maniyyaci wanda bai samu shiga cikin jirgin karshe zuwa Saudiyya ba, ya kaddamar da fara aikin Hajjinsa a sansanin Alhazai da ke jihar Kano, wanda ya ce zai kuma kammala hajjin nasa a sansanin.
Maniyyacin, Malam Jibrin Abdu, daga karamar hukumar Gezawa ya dauki hankalin mutane bayan da aka hange shi sanye da harami wanda ya nuna fara aikin hajjinsa a sansanin alhazan.
- Mahara Sun Sace Basarake Da Matar Aure A Kano
- Hukumar Kashe Gobara A Jihar Kano Ta Ceto Mutum 135 A Watan Yuni
“Ni na fara aikin hajji na tunda akwai dukkan abubuwan da ake bukata a nan, na tabbata zan dawo na kammala aikin, na san yadda ake yi. Wannan ba shi ne zuwana na fari ba, na kuma tabbata ba zai zama na karshe ba,” Inji shi.
Ya kara da cewa, “Na sayar da gonata domin samun zuwa aikin Hajjin, amma wasu shugabannin gangan sun haramta min zuwa hajji,” duk da ya aminta da cewar hakan nufin Allah ne.
Bayan Malam Abdu, ita ma wata mata, Suwaiba Sani, tare da wasu mutane masu yawa, sun yi Allah wadarai tare da dora wannan laifi kan wadanda suka yi sanadin hana su shiga jirgin, wanda cikin fushi suka bayyana cewa ba za su taba yafe wa duk wadanda suke da hannu wajen haramta masu zuwa aikin hajjin ba.
Wakilin LEADERSHIP Hausa a jihar Kano ya nakalto cewa, a kalla maniyyata 745 ne aka bari a kasa a filin sauka da tashin jiragen sama na Malam Aminu Kano a ranar Alhamis bayan da jirgin karshe ya tashi zuwa kasa mai tsarki da misalin karfe 3:45 na yammacin Alhamis din.
Babban sakataren hukumar Alhazai ta Jihar Kano, Muhammad Abba Danbatta, wanda shi ma bai samu tashi a wannan jirgin ba, tare da sauran daraktoci hukumar, ya alakanta wannan matsala da gazawar hukumar alhazan ta kasa bisa rashin cika alkawarin kamfanin da aka yi alkawarin jigilar alhazan na Azman wanda ya sa har sai da Gwamnatin Saudiyya ta kara tsawaita lokacin daukar alhazan amma duk da hakan sai da aka bar wasu da daman.
Kazalika, LEADERSHIP Hausa ta tabbatar da cewa, bayan jihar Kano din, a jihohin kasar nan da dama an samu matsalar jigilar Alhazai inda wasu maniyyata da dama suka rasa damar zuwa hajjin a bana.