An wallafa wata makala a shafin yanar gizo na gidan rediyon muryar Nijeriya (Voice of Nigeria) a jiya Litinin, inda aka ce, yadda kamfanonin Sin suka samar da manhajojin kwaikwayon tunanin dan Adam (AI) na “open source” (masu barin kofar gyara da ba da damar gyara tsare-tsarensu don biyan mabambantan bukatu), ya nuna yunkurin Sin na sa kaimi ga sabuntawar fasahar AI, da samar da karin damammakin hadin gwiwa da bangarorin duniya.
Hakika dimbin kafofin watsa labaru na duniya sun sa lura kan yanayin “open source” na manhajojin AI na Sin. Misali, shafin yanar gizo na Techish na kasar Kenya ya ce, manhajar DeepSeek ta Sin za ta samar da taimako ga kwararru masu tsara manhaja na kasashen Afirka, domin su kirkiro manhajojin da za su biya bukata wajen magance dimbin kalubalen dake fuskantar kasashensu.
- Kantoman Ribas Ya Naɗa Farfesa A Matsayin Sakataren Gwamnati
- Mutane Miliyan 9 Na Iya Kamuwa Da Cutar HIV Saboda Rashin Tallafi
Sai dai, me ya sa aka mai da manhanjojin AI na Sin na “open source”? Dalili shi ne, wannan nau’in manhaja dake iya biyan bukatun karin jama’a na samun karbuwa sosai a kasashe daban daban. Kana yadda karin mutane na kasashen suka fara amfani da manhajar, zai sa a dinga inganta fasahohin da ta kunsa a kai a kai.
Ma’anar aiwatar da matakin “open source” kan manhajojin AI ita ce, maye gurbin tsohon tunani na babakere da son kai, da sabon tunani na tabbatar da bude kofa, da daidaito, da amfanin kowa, da samun ci gaba a kai a kai. Idan mun lakabta wa matakin maye gurbi nan “alamar DeepSeek”, to, za mu iya ganin alamar a manyan harkokin duniya.
A kwanan baya, James Vance, mataimakin shugaban kasar Amurka ya yi jawabi a wajen wani biki cewa, dalilin da ya sa kasashen yamma kirkiro manufar dunkulewar duniya, shi ne domin neman ba kasashe masu sukuni damar samar da kayayyaki masu daraja, wadanda ke kunshe da fasahohin zamani, kana a sanya kasashe marasa karfin tattalin arziki cikin kulawa da ayyukan samar da kayayyaki masu rahusa, wadanda tsarinsu ba shi da sarkakiya. Maganarsa ta nuna niyyar kasashen yamma ta kare tsarin duniya da suka shata, wanda ya kayyade matsayin kasashe marasa karfin tattalin arziki a bangaren samun kudin shiga kadan-kadan, da bin umarnin kasashe masu sukuni.
Sai dai, tabbas za a karya tsarin, ganin yadda ba a samun adalci a ciki. Mun san kasar Sin daya ce daga cikin kasashen da suka warware dabaibayin hana ci gaba da kasashen yamma suka daura musu, inda ta raya tattalin arzikinta, tare da taka muhimmiyar rawa a cikin tsarin duniya ta fuskar samar da kayayyaki.
Daga bisani me kasar Sin ta yi? Ta samar da tunanin gina al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makomar bai-daya, inda aka nanata bukatar ba sauran mutane damar jin dadin zaman rayuwa, matukar wani mahaluki na son samun zaman rayuwa mai inganci. Bisa wannan tunani ne, kasar Sin ta samar da jerin shawarwari masu alaka da ci gaban tattalin arziki, da tsaro, da cudanyar mabambantan al’adu a duniya, da tsayawa kan manufofin tattaunawa tare, da gudanar da aikin gini tare, da raba moriya, gami da sanya kowa a turbar samun biyan bukata, ta yadda kasar ke ta samun amincewa da goyon baya daga karin kasashe.
Tunanin al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makomar bai-daya, da manhajojin AI na “open source”, duk sabbin dabarun daidaita al’amura ne. A lokacin da wani tsohon abu ya gaza biyan bukata, ya kamata a gwada wani na sabo. Ko ba haka ba?(Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp