Rahotonni sun bayyana cewa an gano wasu alamomin cutar shan inna a kananan hukumomi tara na jihar Kebbi, Malamin lafiya na hukumar kula da lafiya a matakin farko na jihar Kebbi, Yusuf Umar Sauwa, ne ya bayyana haka.
Yusuf, ya bayyana haka a yayin wani taron kwana daya da masu ruwa da tsaki suka gudanar a cibiyar bayar da agajin gaggawa ta shan inna da ke Birnin Kebbi.
- Gwamnatin Kebbi Ta Kaddamar da Aikin Gina Tashar Motoci Ta Zamani A Birnin Kebbi
- Wata Kungiya Ta Wayar Da Kan Mutane Kan Dokar Cin Zarafin Jinsi A Jihar Kebbi
Da yake gabatar da bullar cutar ta shan inna da aka gano, a cikin wata gabatarwa da masu ruwa da tsaki da sauran hukumomin bayar da tallafi da ke aiki a jihar.
Yusuf Umar Sauwa ya ce, “An samu rahoton bullar cutar a kananan hukumomi tara na jihar.”
A cewarsa, ana amfani da dabaru da kuma hanyoyin da za a bi domin tunkarar yankunan da cutar ta shafa, ya kara da cewa suna kokarin ganin yadda za su iya dakile yaduwar cutar don ba yara kariyar kamuwa da cutar.
Ya ce, makasudin taron shi ne tattaunawa da jami’an wayar da kan jama’a da masu ruwa da tsaki a jihar, kan samar da hanyoyin da isassun bayanai da za a isar da su ga jama’a, ta yadda za a shiga cikin al’umma don daukar matakan dakile bullar cutar a wasu wuraren. Cewarsa.
Kazalika, za a baiwa al’umma damar shiga domin samun damar cimma manufofin da aka sanya a gaba na magance bullar cutar a yankunan da abin ya shafa.