Dan wasan Super Eagles, Alex Iwobi, ya rubuta sunansa a tarihin gasar Firimiya ta Kasar Ingila, inda ya zama dan Nijeriya na farko da ya ci kwallaye sama da 30 sannan ya taimaka aka ci 30 a gasar ta Ingila, wannan muhimmin lokaci tarihi ya kafu a wasan da Fulham ta doke abokiyar karawarta Liberpool a filin wasa na Craben Cottage a wasan mako na 31 na wannan. kakar.
Iwobi ya yi matukar taka rawar gani a wasan da Fulham ta doke Liberpool da ci 3-2 a ranar Lahadi, babu shakka Iwobi ya kasance fitaccen dan wasa ga Fulham inda ya tabbatar da kansa a matsayin wani kashin bayan kungiyar dake da matukar muhimmanci ga cikar burinta, yanayin taka ledar Iwobi na matukar burge magoya bayan Fulham ya kuma rikitar da tunanin abokan hamayya.
- Yadda Tashar Jirgen Ruwan Apapa-Moniya Za Ta Taimaka Wa Masu Safarar Fitar Da Kaya
- Sin Za Ta Kara Harajin Fito Kan Hajojin Amurka Da Ake Shigarwa Kasar Zuwa 125%
Dan wasan tsakiyar mai shekaru 28 ya jefa kwallo a ragar Liverpool a minti na 32 da fara wasan, hakazalika ya taimaka an cikin minti 5 tsakanin kwallon da ya zura, kwallon da ya ci a wasan ita ce ta 8 da ya ci a wannan kakar wasan ta bana, bajintar da yayi na baya-bayan a gasar Firimiya ya sa kwallayen da ya ci a gasar ta kai 34, sai kuma taimakon da ya bayar aka ci sau 30, abin da ba a taba ganin irinsa ba ga kowane dan wasan Nijeriya a tarihin gasar.
Liverpool ta isa yammacin London ba tare da an doke ta ba a kakar bana, amma gudunsu ya zo karshe ba zato ba tsammani yayin da Fulham ta kara karfi tare da haskakawar Iwobi, dan wasan na Nijeriya da kuma dan wasan baya na Fulham Calbin Bassey sun taimaka matuka wajen samun wannan nasarar akan Liverpool mai dimbin tarihi.
Nasarar ta sa kungiyar Marco Silba ta koma matsayi na takwas a kan teburin gasar Firimiya, inda ta ci gaba da fatan samun cancantar shiga wasannin Turai a badi, yayin da Liberpool ke sake tunani bayan shan kashi da suka yi a hannun Fulham, tarihin da Iwobi ya kafa ba karamar nasara bace ga Nijeriya wanda hakan na nuna irin tasiri da baiwar da Nijeriya ke da shi a fagen tamaula a duniya.
A kowane wasa, tauraron Super Eagles Iwobi na nuna cewa ba wai kawai tarihi yake son kafawa a Duniya ba, ya na sake rubuta labarin ‘yan wasan kwallon kafar Nijeriya a Turai, shan kayen da Liverpool ta yi a Craben Cottage ya jinkirta damarta na lashe gasar Firimiya Lig ta bana.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp