Tun bayan karbar rantsuwar Gwamna Abba Kabir Yusuf a matsayin zababben gwamna Jihar Kano ya fara aiwatar da abubuwan da ya alkawarta wa Kanawa, musamman kan gine-ginen da gwamnatin jihar karkashin Abdullahi Umar Ganduje ta gina.
Domin nuna wa Kanawa da gaske gwamnatin NNPP take tun bayan rantsar da shi, gwamnan ya fara dirar mikiya a filin sukuwa da ke unguwar masu hannu da shuni ta Nasarawa, inda Gwamna Abba ya kaddamar da rushe wasu rukunin kantuna guda 90 da ake zargin na dan Gwamna Ganduje ne.
- Zuba Ruwan Dagwalon Nukiliya Cikin Teku Da Japan Ke Shirin Yi Zai Illata Duk Fadin Duniya
- Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana 12 Ga Watan Yuni, Ranar Hutu
Daga nan ne kuma ya dira a tsohon otal din Daula, wanda Gwamnatin Abba ta zargi Ganduje da yin watandar filin, sai kuma tsohon gidan Jaridar Triump wanda aka tsara mayar da shi wurin kasuwar masu canjin kudaden kasashen waje.
Ita ma kasuwar masaukin alhazai ta gamu da sabon matakin gwamnatin, inda nan ma aka tabbatar da tarwatsa wuraren da aka rabar wa wasu masu kwalli a ido kamar yadda sabuwar gwamnatin ta ce.
Cikin daren Lahadin da ta gabata ce aka dira a filin Idi, inda aka fara ruguje kantinan da ke cikin fili idin kafin wayewar gari aikin gama ya gama.
Wasu na ganin wannan aiki na rusau ya zama babbar barazana ga ‘yan kasuwa da kuma wadanda suka amfana da wasu filayen da gwamnatin baya ta rabar, duk da cewa wannan aiki bai zo wa Kanawa da mamaki ba, domin tun kafin rantsar da Gwamna Abba aka ji yana bayar da sanarwar jan kunne ga duk wanda ke cikin rukunin wuraren da suka shata wa layin rushe su idan suka hau mulki, kamar gine-ginen da aka yi a harabar wasu masallatan Juma’a da na idi, kasuwanni, asibitoci, makarantu, makabartu da ganuwar da ta zagaye birnin Kano.
A ra’ayin wasu, wannan irin aiki ba zai haifar wa Gwamnatin Kwankwasiyya da mai ido ba, musamman ta yadda ake huce haushin kaza kan dami.
Wasu da suka zanta da LEADERSHI Hausa, sun bayyana cewa wannan ba shi ne Kanawa suka zabi Gwamnatin Abba kansa ba, domin mutunen da wannan rusau ya shafa sun yi asarar miliyoyin kudade.
Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya bai wa Gwamnatin Abba shawarar cewa ba haka ya kamata gwamnati ta yi ba, domin kamata ya yi a samar da wani ingantaccen kwamiti ko neman shawarar masana kan yadda ya kamata a fuskanci ire-iren wadannan wurare da ake zargin an raba su ba bisa ka’ida ba.
Ya ce, “Gaggawa aikin shaidan ne, saboda haka akwai bukatar nutsuwa, sannan a yi kokarin duba maslahar al’umma ba yin fushi da fushin wasu ba.”
Wani daga cikin masu rumfuna a masallacin idi, Alhaji Abdurrahaman Yahaya ya bayyana cewa sun kwana cikin mummunan tashin hankali.
Ganau sun tabbatar da yadda aka jibge motocin ruguzau har guda uku a harabar filin idin, yayin da a gefe guda kuma wasu dandazon matasa dauke da kayan aiki ke ta kai wa wasu runfunar farmaki domin kwasar ganima ta hanyar karya kofofin rumfunan da diga.
Yanzu haka dai cikin galibin masu gine-gine a wuraren da za a ruguza ya duri ruwa a kwaryar birnin na Kano, bisa fargarbar yunkurin matasa wadanda ke amfani da wannan dama suna wasoson kayan jama’a, duk da cewa jami’an tsaro na yin bakin kokari, amma dai tun da ita gwamnati take tsaka da wannan aiki nata, hakan ke bai wa matasan karfin guiwar cewa suna lale marhabin da wannan aiki.
Babban koken da al’umma ke yi shi ne, ganin kaso 80 na wadannan gine-gine ba wadanda ake zargi da raba su ne a ciki ba, mafi yawa haya ake a ciki, mutane na ganin cewa ya kamata a bai wa mutane wa’adi domin su samu damar kwashe kayansu kafin a ruguza duk wani gini. Suna ganin cewa ya kamata gwamanati ta ayyana kwace ginin baki daya ta kuma killace shi zuwa lokacin da za ta yanke shawarar abin da ya dace a yi da su, hakan bai samu ba sai gwamnatin ta afka wa ire-iren wadannan wurare cikin dare tare da rakiyar jami’an tsaro.
Yanzu haka akwai wuraren da ake dakon isowar jirgin aikin na Gwamna Abba domin rushewa, misali akwai manyan gidajen mai da ke zagaye da Badala, musamman kan titin zuwa BUK da sauran wuraren da ke jikin makarantu, asibitoci da makabartu, wadanda su ma Gwamna Abba ya sha alwashin dirar masu nan ba da jimawa ba.
Masu sharhin al’amura na ganin rashin alfanun wannan aiki ya fi alfanunsa yawa, musamman idan aka kalli yadda wasu matasa ke amfani da wannan dama suna afka wa dukiyoyin jama’a, sannan kuma jama’a na tsoron kar irin wannan aiki ya zama na ramuwar gayya ta yadda zai zama duk wanda aka sabawa idan ya samu dama irin wannan sai ya yi amfani da ita wajen huce haushi.
Duk da cewa an samu rabuwar kai a kan matakin da gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta dauka na rushe wasu gine-gine da tsohuwar gwamnati ta siyar da filaye. Wasu suna ganin akwai amfani a kan matakin da gwamnan ya dauka, saboda a cewar wasu masu sharhi, gwamnan ya yi nazari sosai kafin daukar wannan mataki, sannan akwai dalilai ko kuma amfanin rushe-rushen kamar yadda suka zayyano.
Nan gaba duk wanda zai sa yi kadarar gwamnati zai tsaya ya tabbatar an bi ka’ida wajen siyar masa, saboda ka da wata gwamnatin ta zo ta kwace ko kuma ta ruguje.
Sannan wannan ruguje-rugujen zai yi maganin matsalolin da ake shiga a gari kamar ambaliyar ruwa idan an siyar da magudanan ruwa.
Zai taimaka wajen ilimintar da al’umma su daina zuba ido gwamnati tana siyar da hakkokinsu a mallaka wa wasu daban.
Har ila yau, zai taimaka wajen ajiye komai a kan gurbinsa, domin gwamnatoci masu zuwa nan gaba za su ji tsoron yin gini a inda bai kamata ba.
Bugu da kari, gwamnatocin da za su zo a gaba za su ji tsoron siyar da wani waje ko bayarwa ga wani mutum daya ko wasu mutane ba tare da bin ka’ida ba ko kuma ta hanyar son zuciya.
Sannan jama’ar gari za su san hakkokinsu, kuma za su ci gaba da sanya ido a kan duk wani waje da gwamnati za ta yanka da sunan fili ko kuma wani waje da gwamnati za ta sayar da sunan samar da hanyar kudin shiga ta hanyar kasuwancin hadin gwiwa tsakanin ‘yan kasuwa da gwamnati.