Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Alfanun Cibiyoyin Da CBN Ya Kafa A Jami’oin Tarayya

by
7 months ago
in SHARHI
3 min read
Alfanun Cibiyoyin Da CBN Ya Kafa A Jami’oin Tarayya
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Daga Jennifer Daniel,

Babban Bankin Nijeriya (CBN) a karkashin Shugabancin Mista Godwin Emefiele ya yi namijin kokari, musamman wajen daga darajar ilimin zamani ta hanyar tattalin arzikin a matsayin daya daga cikin burin da Bankin ya  cimma.

Godwin don cimma wannan manufar ya mayar da hankali, musamman kan matasa ganin cewa sune vangaren da suka yawa a cikin alumma’ar kasar.

Labarai Masu Nasaba

Matsalar Tsaron Jihar Kaduna: Yadda Al’amura Ke Kara Dagulewa

Ko Babban Taron APC Da Na PDP Danjuma Ne Da Danjummai?

Har ila yau, ya kamata a fahimci yadda ya dauki abin a matsayin wani tsari na zakulo matasan musamman daga jamai’a domin ba su horon da ya da ce, inda hakan ya sa ya yanke shawarar kakkafa nagartattun Cibiyoyi a wasu jami’oi mallakar Gwamnatin Tarayya tare da kuma samar da wadatattun kayan aiki don wannan manufar.

Ya samar da ayyukan dalibai na (CBN-CPP) a daukacin jami’oin mallakar Gwamnatin Tarayya da a fadin kasar  musamman don Emefiele  ya ankarr da cewa, jami’oin mallakar Gwamnatin Tarayya na fuskantar matsaloli da dama da suka hada da, karancin kudade lalacewar kayan, rashin cin tashin kai daga sauransu, inda wadannann dimbin matsalolin suka dakele kasar shiga cikin sahun sauran jami’oi da ke a fadin duniya.

Hukumar Webometrics ta duniya da ke fitar da fitar da jeren sunayen jami’oi a duniya wajen ci gaba ta dora Nijeriya Ta shelanta cewa, babu wata jami’a a Nijeriya da ke a cikin jerin jami’oi 1000 manya  a duniya, inda ta ce, babbar jami’ar Ibadan mallakar Gwamnatin Tarayya ce kadai a kan gaba wacce kuma ta shiga sahun manyan jami’oi 1,258 a duniya sannan kuma ta kai mataki na 18 a nahiyar.

An dauki aikin Cibiyoyin na CBN a matsayin wanda ya kai matakin na duniya tare da mayar da hankali ga vangaren ilimin kasuwanci da hada-hadar kudade, lisaafi, a jami’oin da za su amfana.

An fara gudanar da aikin na gwaji a jami’ar Enugu ta Ibadan da kuma ta  Ahmadu Bello Zaria, inda kuma  za a zavo jami’oi shida daga ko wacce shiyyar siysa ta kasar nan.

Babbab Bankin ya zuba wuri na gugar wuri a cikin aikin har naira biliyan 63 a wadannann Cibiyoyin tara mallakar Gwamnatin Tarayya domin samar da ilimin a karkashin shirin horas a da daliban na (TIES).

A yayin da yake kaddamar  Cibiyar ta Ahmadu Bello a kwanan baya  Emefiele, ya shelanta cewa, na daya daga cikin daukin day CBN ya samar don kara daya darajar vangaren ilimin zamani a kasar.

Ya ci gaba da cewa, Cibiyoyin za a kakkafa a kashi -kashi na aikin, inda kuma aka kammala Cibiyoyin a jami’oin Ibadan da kuma ta Ahmadu Bello wadanda jami’oin a yanzu, za su iya yin amfani da su.

Ya kara da cewa, sauran aikin Cibiyoyin a jami’oin Lagos, Fatakwal, Jos, Bayero da kuma ta  Maiduguri ana dad da Kammala su.

A cewar Emefiele, an kuma samar da dakin fa zai dauki mutum 500, kayan aikin ICT da kuma dakin karatu na zamani da za su iya gudanar da aiki kafada-da kafada da irin na makarantun koyon darasin kasuwanci a duniya.

Misali, Cibiyar ta jami’ar Ahmadu Bello an samar da kujerun zama 360, an samar da wasu dakuna, dakunan gudanar da tarruka bakwai da wasu dakuna ahida, inda hakan ya kai, jimmalr da zai ci mutum 544, har da kuma samar da wasu azuwan da za su dauki dalibai 240.

Har ila yau, ana samar da dakin cin abinci mai hada da madafi da zai iya daukar kujeru 96, ofis-ofis 32 da ma’aikata 59 za su zauna, samar da dakin karatu da zai dauki kujeru 68 da kuma samar da kujerun mutum  50 za su yi amfani da su.

An kuma samar da dakunan kwana da suka kai dakuna dai-dai 66 da kuma masu daukar mutane da yawa guda 33, inda a dakin kwanan, an kuma samar da wajen motaa jiki wasu dakunan hutawa bakwai, dakunan taro biyu dakunan wanki 13, dakuna sadarwa biyu da kuma wasu manyan dakuna taro biyu, an kuma tanadi dakin ajiye Janereta biyu mai karfin 1100KVA, na’urar tarafoma biyu IMVA kayan kashe gobara biyu, na’urar sanyaya daki da sauransu.

Emefiele  ya bayyana cewa, Bankin ya shigo ne domin samar da dauki ga fannin ilimin zamani na kasar, inda ya kara da cewa, an kuma samar da aikin ne, domin zakulo kwarrun dalibai sa za su yi amfani da ilimin zamani fa suka samu don a kara bunkasa ilimin tattalin arzikin kasa ta hannyar yin amfani da ilimin kirkire-kirkire,musamman don Nijeriya ta kai babban mataki a fannin kasuwanci a nahiyar Afirka.

Ya ci gaba da cewa, an kuma yi nazari kan aikin don ganin an cimma burin da aka sa a gaba, musamman wajen ganin kasar ita ma ta kai mataki na duniya a fannin koyon darusan kasuwanci, inda ya yi nuni da cewa, Cibiyoyin za su taimaka matuka wajen rage dalibai ma su zaman kashe wando bayan sun kammla jami’a a kasar.

Kwarrun da aka sa a cikin gudanar da aikin suna da yakin cewa, jami’oin da aka zavo za su amfana da Cibiyoyin,  musamman wajen gudanar da ayyukan su dai dai da yadda jami’oin da ke yankin New York da na kasar Dubai ke bayar da horo a fannin koyon darasin aikin banki,  hada-hadar kudade fa sauransu.

Daniel mai yin faahin baki ne a vangaren zuba hannun jari da ke zaune a jihar Kaduna.

 

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

 Dalilan Yawaitar Mutuwar Aure A Wannan Zamanin

Next Post

Ina Da Kyakyawar Alaka Da Kowa Da Kowa A Kannywood —Saratu Gidado (Daso)

Labarai Masu Nasaba

Matsalar Tsaron

Matsalar Tsaron Jihar Kaduna: Yadda Al’amura Ke Kara Dagulewa

by Bello Hamza and Shehu Yahya
1 month ago
0

...

Taron

Ko Babban Taron APC Da Na PDP Danjuma Ne Da Danjummai?

by Bello Hamza and Idris Aliyu Daudawa
2 months ago
0

...

Masoya

Bikin Ranar Masoya Ta Duniya A Mizani

by
3 months ago
0

...

Noman Rogo

Kokarin CBN Wajen Sake Farfado Da Noman Rogo A Nijeriya

by
3 months ago
0

...

Next Post
Kannywood

Ina Da Kyakyawar Alaka Da Kowa Da Kowa A Kannywood —Saratu Gidado (Daso)

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

%d bloggers like this: