Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya bayyana cewa zai samar da kuɗin ƙasashen waje mai rangwame (BTA) ga masu niyyar zuwa aikin Hajji na 2025 ne kawai ta hanyar katin biyan kuɗi (ATM) sakamakon tsarin da ya ɓullo da shi wajen bayar da BTA.
Sai dai, CBN ya shawarci hukumomin Hajj na Nijeriya da su nemi dalar Amurka a kasuwar bayan fage domin samun kuɗin da za su yi amfani da shi a ƙasa mai tsarki, saboda a cewar CBN ba shi da wadatacciyar dala a rumbun ajiyar kuɗi na gwamnati don masu aikin Hajji.
- CBN Ya Sahale Wa Masu Musayar Kudade Sayen Dala 25,000 A Mako
- Majalisa Ta Bukaci CBN Ya Gaggauta Dakatar Da Karin Caji A ATM
Wata majiya daga hukumar aikin Hajji ta Nijeriya (NAHCON), ta bayyana wa HAJJ REPORTERS cewa sauya tsarin bayar da BTA daga kuɗi a hannu zuwa katin biyan kuɗi na ATM zai haifar da matsala mai girma ga masu aikin Hajji na 2025.
A cewar majiyar, “Mun tattauna da CBN akan wannan batun, kuma sun ce wannan ya na cikin tsarin su wanda ba za a iya sauyawa ba, saboda hakan zai buɗe kofa ga wasu hukumomi su ma su nemi hakan. Sun ce ko dai mu karɓi katin ko mu nemi dalar a kasuwar bayan fage, kuma kuna sane da abinda hakan zai haifar.”
Har yanzu dai hukumar kula da alhazzai ba ta bayar da wata sanarwar a hukumance kan wannan batu ba kawo yanzu da muke haɗa wannan rahoto.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp