Shugaban ma’aikatar kula da fina-finai da nishadi ta Nijeriya, kuma fitaccen jarimi a masana’antar Kannywood, Ali Nuhu ya zama jakadan kamfanin tsaftace hakora a Arewacin Nijeriya.
An bayyana Ali Nuhu ne a matsayin jakadan kamfanin a yayin kaddamar da bikin kasuwanci na Kamfanin da aka yi a kasuwar Bata da ke Jihar Kano, a ranar Asabar, 30 ga watan Nuwamba, 2024.
- Gwamnoni Sun Miƙa Ta’aziyya Ga Waɗanda Wani Abu Ya Fashe Da Su A Mota A Zamfara
- Adadin Zirga Zirga Ta Jiragen Kasa A Sin Ya Haura Biliyan 4 A Watanni 11 Na Farkon Bana
Da yake jawabi a lokacin kaddamarwar, Manajan tallace-tallacen kamfanin Colgate na yankin Arewa, Abdul Musa, ya bayyana cewa, zabar Nuhu ta samo asali ne saboda karbuwa da kuma shahararsa a Arewa, bisa la’akari da rawar da yake takawa a harkar fina-finan Nijeriya.
Musa ya lura cewa, Nuhu ya kasance mafi dacewa don sadarwa da inganta mahimmancin kula da baki mai kyau da kuma fa’idojin amfani da samfuran Colgate ta hanyar da ta dace da masu amfani na cikin gida.