Attajirin ɗan kasuwar nan wanda yafi kowa kuɗi a nahiyar Afrika, Alhaji Aliko Dangote, ya sauka daga muƙaminsa na Shugaban hukumar Kamfanin Dangote Sugar Refinery Plc, wanda ya riƙe sama da shekaru ashirin. Wannan mataki ya kawo ƙarshen dogon shugabancin da ya sauya fasalin kamfanin ya zama jagora a harkar sarrafa sukari a Nijeriya.
Wata sanarwa daga Sakataren Kamfanin, Temitope Hassan, ta tabbatar da cewa saukar Dangote zai fara aiki daga ranar 16 ga Yuni, 2025. Tun daga 2005 yake jagorantar hukumar, inda ya kula da bunƙasar kamfanin da kuma aiwatar da sabbin tsare-tsare na shugabanci da ingantattun ƙa’idojin gudanarwa.
- Ɗan Ƙasar Indiya Da Wasu 12 Sun Gurfana A Kotu Kan Satar Wa Dangote Dizal Na Naira Biliyan 4
- Hako Man Fetur: Jihar Neja Ta Nemi Hadin Gwiwar Kamfanin Dangote
A ƙarƙashin jagorancinsa, kamfanin ya fara manyan ayyukan Backward Integration Projects (BIP) a jihohin Adamawa, Taraba da Nasarawa domin bunƙasa samar da sukari a cikin gida tare da rage dogaro da shigo da kaya daga waje.
Bayan nazari mai zurfi da tsari na sauyin shugabanci, hukumar ta bayyana naɗin Mr. Arnold Ekpe, tsohon Shugaban Ecobank kuma mamba mai zaman kansa a hukumar, a matsayin sabon Shugaban Kamfanin, wanda zai fara aiki daga 16 ga Yuni, 2025.
Hukumar ta gode wa Dangote bisa shugabanci mai nagarta da sadaukarwa da ya nuna tsawon shekaru, tare da maraba da sabon shugaban kamfanin, Mr. Ekpe, wanda ke da gogewa mai zurfi a harkar banki da shugabancin manyan ƙungiyoyi a nahiyar Afrika.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp