Kwanan nan, babbar kwamishinar MDD mai kula da harkokin hakkin bil Adam Madam Michelle Bachelet ta kawo karshen ziyararta a kasar Sin.
A gun taron manema labarai da aka gudanar, Madam Bachelet ta bayyana abubuwan da ta gani da idonta a yayin ziyarar, inda ta jaddada cewa, ta tuntubi sassa daban daban ba tare da an sanya mata ido ba, furucin da ya karyata jita-jitar da ‘yan siyasar Amurka da na kasashen yamma suke kokarin yadawa dangane da Xinjiang, wadanda har suka bukace ta da yi murabus daga mukaminta.
Shafawa kasar Sin bakin fenti bisa wai “batun Xinjiang” don neman dakile ci gaban kasar, ba wani boyayyen abu ba ne ga Amurka da kawayenta. Rahoton na cewa, jami’an karamin ofishin jakadancin Amurka a birnin Guangzhou na kasar Sin, Sheila Carey da Andrew Chira, sun bayyana wa baki a wata liyafa a shekarar 2021 cewa, gwamnatin Amurka tana fatan ‘yan kasuwan Amurka su fahimci cewa, batun aikin tilas da na kisan kare dangi da ake yayatawa kan jihar Xinjiang, “mataki ne da ya dace” a yunkurin da ake yi na “jefa gwamnatin kasar Sin cikin mawuyacin hali.” Shi ma Lawrence Wilkerson, babban jami’in tsohuwar gwamnatin Amurka ya bayyana a shekarar 2018 cewa, mataki mafi kyau ga Amurka wajen lahanta kwanciyar hankalin kasar Sin, shi ne tada zaune-tsaye a jihar Xinjiang, don kawo wa kasar matsala a cikin gidanta.
“Tilasta wa ‘yan kabilar Uygur yin aiki” da “yi musu kisan kare dangi”, laifuffuka ne da Amurka da kawayenta suka dora wa kasar Sin, amma karya fure take ba ta ‘ya’ya. Cikin shekaru sama da 70 da suka wuce, yawan ‘yan kabilar Uygur mazauna jihar Xinjiang ya karu daga miliyan 3.6 zuwa miliyan 11.6, kwatankwacin yadda Indiyawan daji ‘yan asalin Amurka suka ragu matuka cikin shekaru 400 da suka wuce, daga miliyan 5 zuwa dubu 250 a farkon karni na 20.
Mene ne gaskiyar lamarin? To, alkaluma sun bayyana a zahiri.
Kasar da ta zo ta farko wajen yawan mamata a sanadin annobar Covid-19, wadda kuma ke fama da yawan harbe-harben bindiga da matsalar bambancin launin fata, muna ba ta shawarar mai da hankali a kan matsalar cikin gidanta maimakon shafawa wasu bakin fenti. (Mai Zane:Mustapha Bulama)