A yau Jumma’a, kungiyar kula da aikin zirga-zirga da sayo kayayyaki ta kasar Sin wato CFLP ta gabatar da alkaluman adana kaya na watan Mayu na kasar Sin, inda suka nuna cewa, ana tafiyar da sana’o’i masu nasaba da adana kaya cikin himma da kwazo, kana, bukatar al’umma a wannan fanni tana ci gaba da karuwa, lamarin da ya shaida yadda sana’o’in ke bunkasuwa kamar yadda ake fata.
Alkaluman adana kaya na watan Mayu na kasar Sin ya kai kaso 50.5 bisa dari, wato ya fadada cikin watanni 7 a jere da suka gabata. Kana, alkaluman sabbin oda na ci gaba da karuwa.
A sa’i daya kuma, bukatun adana kayayyakin yau da kullum sun karu sakamakon karuwar bukatun al’umma na sayen kayayyaki yayin bukukuwa, lamarin da ya sa, alkaluman sabbin oda da ke shafar abinci, amfanin gona, kyayyakin gida masu amfani da wutar lantarki suka karu sosai. (Mai Fassara: Maryam Yang)














