Gwamnatin Sin ta gabatar da karuwar GDPn kasar na rabin farkon bana na kashi 5.3% a jiya Talata, inda kafofin yada labarai na duniya suka ce bunkasuwar tattalin arzikin Sin ya zarce hasashen da aka yi.
Ban da alkaluman da aka bayar a bangaren bunkasuwar tattalin arziki, alkaluman samun guraben aikin yi da farashin kayayyakin masarufi da kuma kudaden da aka samu ko aka kashe a duniya su ma muhimman ma’aunai ne dake kimanta yadda tattalin arziki ke tafiya. Tun farkon shekarar bana, yawan rashin ayyukan yi da farashin kayayyakin masarufi ba su karu ba, inda a watan Yunin da ya shude, alkaluman kudin da ake kashewa na sayen kayayyaki CPI, suka daidaita tare da samun ’yar karuwa ta kashi 0.1%. An kuma samu daidaito tsakanin kudaden da ake samu da kashewa a duniya, inda yawan kudaden waje da Sin ta adana ya kai fiye da dala triliyan 3.2. Dukkan alkaluman na bayyana bunkasuwar tattalin arzikin Sin ba tare da tangarda ba, matakin da ya aza tubali mai inganci ga bunkasuwar tattalin arziki a rabin karshen shekara.
Abu mafi jawo hankali shi ne, yawan kudin dake shafar cinikin shige da fice a nan kasar Sin a rabin farkon bana ya kai kudin Sin Yuan triliyan 21.79 kwatankwacen dalar Amurka fiye da triliyan 3, adadin da ya karu da kashi 2.9% bisa na makamancin lokacin a bara, kuma ya kai matsayin koli a tarihi, abin ya bayyana ingantaccen karfin tattalin arzikin Sin.
Karfi mai inganci da tattalin arzikin Sin ke bayyanawa na sanarwa duniya cewa, Sin kasa ce mai ba da tabbaci da ingiza bunkasuwar tattalin arzikin duniya gaba, kuma za ta more damammakinta da daukacin duniya. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp