Dan takarar shugaban kasa a inuwar jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana irin alkawarukan da zai yi wa ‘yan Nijeriya kan tsaro, zaman kashe wando da kuma bunkasa tattalin arziki, idan har ya zama shugaban Nijeriya a 2023.
Ya ce manufofinsa suna da matukar muhummanci kuma ya ki bayyana ne tun da wuri saboda kar sauran ‘yan takara su yi satan amsa.
- Alhassan Doguwa Ya Musanta Samun Sabani Tsakaninsa Da Ganduje
- Kotu Ta Soke Zaben Fidda Gwanin PDP A Kaduna Ta Tsakiya, Ta Bada Mako 2 A Sake Wani Zaben
“Mun jirkinta fito da manufofinmu ne saboda kar sauran ‘yan takara su yi satan amsa. Manufofinmu suna da matukar muhummanci, domin haka ne muke kira ga ‘yan Nijeriya su karanta da kyau tare da yin nazari a kai. Muna bukatar ‘yan Nijeriya su dunga kallon wadannan manufofi a matsayin yarjejeniya tsakanin Kwankwaso/Idahosa da kuma mutane,” in ji shi.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne a lokacin da yake bayyana manufofinsa a Abuja ranar Talata da ta gabata, inda ya ce zai fi mayar da hankali ne kan tsaro, ilimi, lafiya, sake fasalin kasa dsa kuma muhalli da dai sauransu.
Tsohon gwamnan Jihar Kano ya kara da cewa zai sake maimaita abubuwan da ya yi a Kano wajen kafa kwamiti mai mutum 11 a gunduma da karamar hukuma da kuma matakin tarayya a matsayin hanyan magance rashin tsaro da sauran matsaloli da suka addabi mutane.
Ya kuma ce gwamnatinsa za ta farfado da fasahar zamani wajen ceto Nijeriya, inda ya ce akwai hanyoyin da ake bi wajen tsare kasa daga farmakin cikin gida da na waje.
A cewarsa, zai bai wa hazakun mutane manya-manyan mukamai domin gudanar da aiki yadda ya kamata a kowani bangare.
“A cikin gwamnatinmu, babu wani yaro a Nijeriya da za a hana masa rubuta jarrabawan WAEC, NECO, JAMB da dai sauransu, saboda gwamnati ce za ta biya musu kudin rajista. Wadannan jarrabawa za su kasance kyauta ne, sannan duk wani fom na shiga babban makaranta zai kasance kyauta ne.
“Wadannan hukumomin jarrabawa za su kasance kyauta ne a karkashin gwamnatin Kwankwaso.
“Sakamakon jarrabawa ta JAMB a karkashin gwamnatin Kwankwaso zai kasance na tsawon shekaru hudu kafin wa’adin jarrabawar ya kare,” in ji shi.
Har ila yau, Kwankwaso ya yi alkawarin sake shigar da yara makaranta wadanda aka kora a fadin kasar nan ta hanyar gina ajujuwa 500,000 a dukkan kananan hukumomin Nijeriya guda 774.