Tun bayan dawowar mulkin dimokuradiyya a shekarar 1999, majalisun dokokin Nijeriya sun shafe shekara 25 ba tare da wata tangarda ba, inda suka amince da kudirorin 800 wanda suka zama doka. Za mu duba kudirori guda 10 wadanda suka sauya alkiblar dimokuradiyyar Nijeriya da majalisar dattawa da ta wakilai suka amince har suka zama doka.
Mafi yawan ‘yan majalisa suna da ra’ayin cewa, majalisa ita ce bangaren gwamnati da aka fi rashin fahimta. Wannan lamari ya samo asali ne daga kakkausar da ‘yan kasa suke musu akai-akai, musamman dangane da yawan albashin da ake ba su.
Lallai majalisa ita ce bangaren da ta fi sauya alkiblar dimokuradiyyar Nijeriya.
A majalisa ta 4 tsakanin 1999 zuwa 2003, majalisar dattawa ta zartar da kudurori 65, yayin da majalisar wakilai ta zartar da kudirori 112, amma ‘yan majalisa na dukkan zauren majalisun biyu sun samu daidaito ne a kudurori 65.
An sami ci gaba sosai a majalisar ta 5, lokacin da aka zartar da kudurori 129. Adadin ya ragu zuwa kudirori 72 a majalisar ta 6, ya haura zuwa 128 a majalisar ta 7, ya kuma kai matsayin da ba a taba gani ba na kudirori 282 a majalisar ta 8, kafin daga bisani ya koma 134 a majalisa ta 9.
Ga wasu daga cikin kudirori da suka sauya alkiblar dimokuradiyyar Nijeriya kamar haka:
Kudirin Dokar Man Fetur (PIA)
Bayan shafe shekara da shekaru ana kai ruwa rana, kudirin dokar man fetur ya samu amincewa a 2021, bayan da tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya rattaba masa hannu. An dai fara gabatar da kudirin dokar a majalisa ne tun a 2008.
Kudurin dokar zai taimaka wa bangaren masana’antar man Nijeriya wajen samar da tsarin hanyoyin samar da kudade da shugabanci da wasu batutuwa a wannan fannin.
Majalisar dattijai ta 9, ta zartar da kudirin dokar a ranar 15 ga watan Yulin 2021, yayin da majalisar wakilai ta yi hakan a ranar 16 ga watan Yuli, wanda hakan ya kawo karshen dogon jira da bai wa masana’antar man fetur ta Nijeriya wata sabuwar alkibla da ake sa ran zai kawo ci gaba a kasar.
Kudirin Dokar ‘Yancin Bayanai (FOI)
Kudurin dokar ‘yancin bayanai wata doka ce da ta goyi bayan bin diddigi da shugabanci nagari. Kudirin dokar na neman kara inganta wa al’ummar Nijeriya tsarin dimokuradiyya ta hanyar bai wa ‘yan kasa ‘yancin samun bayanan na ma’aikatun gwamnati. An fara gabatar da kudirin dokar ne tun a shekarar 1999, an yi gyare-gyare da tattaunawa da dama har sai da tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya sanya hannu kan kudirin dokar a ranar 28 ga Mayun 2011. Kudurin dokar ‘yancin bayanai kamar yadda aka san kowacce doka tana tabbatar wa mutane ‘yancin samun bayanau da ke hannun gwamnati.
‘Yan jarida da lauyoyi da kungiyoyin fararen hula suna amfani da wannan kudirin doka wajen titse jami’an gwamnati da ma’aikatu wajen bin diddigin ayyukansu. Duk da haka dai, akwai matsala game da rashin bin tsarin wannan doka ga wasu ma’aikatun gwamnati.
A shekarar 2021, majalisar wakilai ta ce cibiyoyin gwamnati 73 ne kawai daga cikin 900 da ke kasar ke yin aiki da tanadin dokar ‘yancin yada labarai (FOI) kan bayyana bayanai.
Kudirin Dokar Haramta Auren Jinsi
Wannan kudirin doka ne da majalisar dokoki ta kasa ta amince da ita, kuma gwamnatin Goodluck Jonathan ta amince da ita, bisa ga matsin lamba daga gwamnatocin kasashen Yamma na mutunta ‘yancin ‘yan luwadi da madigo.
A ranar 29 ga Nuwambar 2011, majalisar dattawa suka amince da kudirin dokar haramta auren jinsi. Haka a ranar 30 ga Mayun 2013, majalisar wakilai ta amince da kudirin dokar haramta auren jinsi. A watan Janairun 2014 ne Jonathan ya rattaba wa kudirin dokar hannu ta zama doka. kafin wannan lokaci, kudurorin doka irin wannan guda biyu ne aka gabatar a zauren majalisa a 2006, amma ba su samu karbuwa ba.
Kudirin dokar ya haramta auren luwadi, ya kuma haramta kungiyoyin da ke goyon bayan ‘yancin ‘yan luwadi, da kuma tanadar daurin shekara 14 ga wanda aka kama da laifin.
Sakamakon koma-bayan da aka samu, masana harkokin siyasa da dama sun yi Imani da cewa sanya hannu kan kudirin dokar zai fusata kasashen yammacin Turai, wanda suka dauki matakai kan Nijeriya ciki har da kin sayar mata da makamai duk da irin barnar da kungiyar Boko Haram ke yi a wannan lokaci. Wasu na ganin hakan ma ya taka muhimmiyar rawa wajen kayar da gwamnatin Jonathan a 2015.
Kudirin Dokar Bai Wa Matasa Damar Yin Takara
Majalisar dokokin Nijeriya ta zartar da kudirin dokar don sauya sashe na 65, 106, 132, da 177 na kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999 da aka yi wa kwaskwarima. Dokar ta sassauta wasu tsauraran matakai na kundin tsarin mulkin kasar. Ya rage shekarun cancantar tsayawa takarar shugaban kasa daga 40 zuwa 30, gwamnoni daga 35 zuwa 30, Sanatoci daga 35 zuwa 30, ‘yan majalisar wakilai daga 30 zuwa 25, da ‘yan majalisun jihohi daga 30 zuwa 25.
A watan Yulin 2017, majalisar dokoki ta amince da kudirin dokar kuma aka mika shi don amincewa a watan Afrilun 2018. A ranar 31 ga Mayu, 2018, sai tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya sanya hannu. Tun daga wannan lokacin, dokar ta bai wa matasa da dawa damar tsayawa takarar majalisa.
Kudirin Dokar Kyamar Nakasassu
Kudirin dokar da ke da nufin kawar da wariya ga nakasassu, an zartar da shi ne a shekarar 2016. Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya sanya wa kudurin dokar hannu a ranar 23 ga Janairun 2019.
Dokar ta haramta duk wani nau’i na nuna wariya kan nakasa kuma an sanya tarar naira miliyan 1 ga kungiyoyin da kuma naira 100,000 ga daidaikun mutane, ko kuma zaman daurin watanni shida a gidan yari ga duk wanda aka kama da cin zarafin nakasassu.
Kudirin Dokar Kariya Ga Masu Fallasa Cin Hanci
A watan Yulin 2017, majalisar dattawa karkashin jagorancin Bukola Saraki, ta amince da kudirin dokar kariya ga masu fallasa cin hanci da rashawa.
Kudirin dokar ya bai wa wadanda ke fallasa masu cin hanci da rashawa kariya daga duk wata barazana da sa iya fuskanta. Gwamnatin tarayya ta amince da kudirin dokar ne domin yakar cin hanci da rashawa a ma’aikatun gwamnati.
Kudirin Dokar Kiwon Lafiya
Majalisa ta 7 ce ta amince da kudirin dokar kiwon lafiya, wanda tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya rattaba wa hannu a watan Disambar 2014.
Kudirin dokar ya bayyana rawar da matakan gwamnatin uku za su iya takawa kan batutuwar da suka shafi kiwon lafiya. Ana sa ran kudirin dokar zai taimaka wa ‘yan Nijeriya wajen samun ayyukan kiwon lafiya da inganta fannin lafiya da samar da kwarru kan fannin lafiya.
Kudirin Dokar Bai Wa Dalibai Bashi
Majalisa ta 9 ce ta amince da kudirin dokar bai wa dalibai bashi, wanda Femi Gbajabiamila ya gabatar a zauren majalisa.
A ranar 12 ga Yunin 2023, Shugaban kasa, Bola Tinubu ya rattaba hannu kan kudirin dokar bai wa dalibai bashi, domin bai wa daliban Nijeriya damar samun bashi mara ruwa wajen gudanar da harkokin karatunsu.
Kudirin Dokar Mafi Karancin Albashi
Bayan kan ruwa rana da gudanar da zanga-zanga da kuma tattaunawa tsakanin kungiyar kwadago da gwamnatin tarayya na tsawon shekara 2, majalisar dattawa ta amince da kudirin dokar mafi karancin albashi na naira 30,000 a 2019, tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya rattaba wa kudirin dokar hannu kuma ya bayar da umurnin a fara aiki da ita tun daga ranar 18 ga Afrilun 2019. A yanzu haka akwai sabuwar takaddama kan mafi karancin albashi.
Kudirin Dokar Kirkiro Hukumar NEDC
Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a kan kudirin dokar kafa hukumar raya arewa maso gabas (NEDC) na shekarar 2017, a watan Oktoban 2017, bayan da majalisar dokokin Nijeriya ta amince da shi.
Ana kallon kudirin dokar kafa NEDC a matsayin warware matsalolin yankin arewa maso gabas sakamakon barnan da kungiyar Boko Haram ta yi a yankin.
Bayan kafuwar hukumar, tana da hurumin karba da sarrafa kudaden da gwamnatin tarayya da kungiyoyin bayar da agaji na kasa da ksa ke ware domin sake tsugunar da mutanen yankin da gyarawa da gina sabbin hanyoyi da gidaje da wuraren kasuwanci wadanda rikicin ya rutsa da su.
Majalisar dattawa ta zartar da kudirin ne a watan Oktoban 2016, don samun wani bangare na kashi uku na harajin da aka kara wa gwamnatin tarayya.