Tsohon dan majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Birnin Kano, Hon. Abubakar Nuhu Danfulan Danburan ya bayyana cewa Allah ya yi wa Alhaji Aminu Dantata arzikin da al’umma suka amfana da shi.
Ya ce, “Wannan rashi da aka yi na Alhaji Aminu Dantata, rashi ne babba na Uba, shugaba, abin alfahari gare mu, ba rashi ba ne ga Jihar Kano ita kadai ba har da kasa baki daya da al’ummar musulman duniya wannan rashi ya shafesu gaba daya, Allah ya gafarta masa ya ba shi aljanna”
- Ƴan Bindiga Sun Yi Wa Jami’an NSCDC Ƙwantan Ɓauna A Binuwe
- Sojoji Sun Kai Hari Maɓoyar Boko Haram A Borno, Sun Kashe Wasu ‘Yan Ta’adda
Hon Abubakar ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da ‘yan jarida.
Ya ce shi ne irin mutumin da ake cewa Allah ya yi masa arziki wanda kowa zai yi fata ya yi koyi da irin abubuwan da ya yi na rayuwa a duniya da arzikinsa da wadatarsa sun amfani ba wai kawai ga iyalansa, jikokinsa ko surukansa ba har al’umma da ‘yan’uwa da abokan arziki da kuma al’ummar musulman na duniya.
Ya kara da cewa domin ya amfanar da abubuwa da yawa na taimakon da ya yi, wanda sai yanzu ne wasu suke ta fitowa, ya yi wasu abubuwa tsakaninsa da Allah, daya daga cikin sakamako da wannan abubuwa suka haifar masa shi ne, na yadda aka yi jana’izarsa a Madina kusa da Annabi, wannan ba karamar daraja ba ce Allah ya nuna masa tun daga duniya.
Hon Abubakar ya ce ba zai taba mantawa ba haduwarsu da Alhaji Aminu Dantata na karshe ita ce ranar karamar Sallah, ya je wajensa a Makka bayan an kammala Azumi, a nan ya yi idi, shi kuma Allah ya kai shi Makka a wannan lokaci da ma duk shekara yakan kai masa ziyara ya gaishe shi, wani abin ban sha’awa a rayuwarsa duk da yawan shekarunsa, Allah bai sa baya gane jama’a ba, yana da lafiyar yin magana ga mutane har ya janyo barkwanci.
Ya ce baiwar da Allah ya yi wa Aminu Dantata na gane jama’a a tsawo shekaru sama da 90, ba karamar baiwa ba ce, sai dai kullum abin da yake fada mana shi ne, “ku saka hakuri a rayuwa ku, ku zama mutane masu rike amana da gaskiya duk abin da za mu yi, mu yi don Allah, mu tsaya mu taimaka addininmu”.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp