Allah ya yi wa fitaccen tsohon dan wasan kwaikwaiyon nan na arewacin Najeria, Alhaji Usman Baba Pategi wanda da aka fi sani da Samanja Mazan Fama, rasuwa.
Samanja ya rasu ne daren ranar Lahadi bayan ya sha jinya. Marigayi Samanja ya rasu yana da shekaru 81 a duniya.
- Zababben Dan Majalisar Jiha Mai Wakiltar Chikun Ta Jihar Kaduna Ya Rasu
- Diphtheria: Mutum 3 Sun Rasu, An Kwantar Da 7 A Asibiti A Kaduna
Alhaji Usman Baba Pategi ya taka rawa a matsayin Samanja Mazan Fama a wasan kwaikwaiyon da aka kwashe shekara da shekaru ana gabatarwa a Gidan Rediyon Nijeriya na Kaduna.
An haife shi a ranar 20 ga watan Mayu na shekarar 1942 a Masarautar Pategi da ke Jihar Kwara.
Ɗa ne ga marigayi Etsu Usman Patako na Pategi.
Usman Baba Pategi ya yi karatun Firamare da Sakandare a Pategi da Ilorin.
A shekarun 1960 ya shiga Rundunar Sojin Nijeriya inda ya rike mukamin Kyaftin a lokacin yakin basasar kasar.
Ya yi ritaya a shekarar 1985 inda ya soma wasan kwaikwayo a Gidan Rediyon Nijeriya na Kaduna, lamarin da ya ba shi damar rubutawa da kuma bayar da umarni na wasannin kwaikwayo. An fi saninsa a matsayin Samanja Maza Fama.
Baba Pategi ya rasu ya bar mata biyu da ‘ya’ya.
Za a yi jana’izarsa yau Lahadi 12/11/2023 da misalin karfe 10 a gidansa da ke Kabala Costain jihar Kaduna.
Muna addu’ar Allah ya gafarta masa, ya kula da bayansa.