An samu bullar Diphtheria a karamar hukumar Makarfi ta jihar Kaduna inda ta yi ajalin wasu yara uku da keantar da bakwai a asibiti.
Malam Aliyu Alassan, sakataren lafiya na karamar hukumar Makarfi, ya tabbatar da hakan a ranar Asabar a Jihar Kaduna.
- Gwamnatin Kaduna Ta Tabbatar Da Bullar Cutar Diphtheria A Kafanchan
- Diphtheria: Mutane 123 Sun Kamu, 38 Sun Mutu A Jihohi 4 – NCDC
Alassan ya ce akasarin wadanda abin ya shafa yara ne.
“Wadanda ake zargin suna dauke da cutar an kai su asibiti an kebe su domin duba lafiyarsu.
LEADERSHIP ta rawaito cewa a kwanakin nan ma’aikatar kula da lafiya ta jihar ta tabbatar da bullar cutar Diphtheria a yankin Kafanchan, hedikwatar karamar hukumar Jema’a ta jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp