Alhaji Abbas Sanusi, Galadiman Kano, ya rasu kamar yadda Leadership Hausa ta samu rahoto.
An yi jana’izarsa da misalin ƙarfe 10 na safe a Ƙofar Kudu da ke Kano.
- Kano Pillars Ta Janye Dakatarwar Da Ta Yi Wa Kocinta, Usman Abdallah
- Gwamnatin Edo Za Ta Biya Diyyar Mafarauta ‘Yan Kano 16 Da Aka Kashe A Uromi
Marigayin shi ne kawun Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, kuma mahaifin Abdullahi Abbas, shugaban jam’iyyar APC na Jihar Kano.
Kafin naɗa shi matsayin Galadiman Kano, ya riƙe sarautar Wamban Kano kuma yana daga cikin manyan masu faɗa a ji a Majalisar Sarakunan Kano.
Rasuwarsa babban rashi ne ga sarautar gargajiya a Kano.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp