Allah ya yi wa fitacciyar jarumar Kannywood Saratu Gidado wadda aka fi sani da Daso rasuwa.
Labarin rasuwar ya karade gidajen rediyon Kano, inda lamarin ya motsa zukatan jama’ar jihar Kano.
- Kannywood Wuri Ne Na Nishadi Ba Gyaran Tarbiyya Ba -Fauziyya D Suleiman
- Ali Nuhu: Shekara 50 Masu Dauke Manyan Nasarori
‘Yan uwanta sun ce, Daso ta rasu ne a yayin barcinta na daren Talata bayan ta ci abincin Sahur.
Daso dai, fitacciyar jaruma ce a masana’antar fina-finan Hausa wacce ta shafe fiye da shekaru 18 a masana’antar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp