Gwamnatin Jihar Bauchi ta sanar da rasuwar Alhaji Abubakar Jafaru Ilelah, Wakilin Sadarwan Bauchi, wanda ya rasu a ranar Talata bayan ya yi rashin lafiya.
Kwanan nan, gwamnan Jihar Bauchi ya naɗa Jafaru Ilelah a matsayin mai ba shi shawara kan harkar wayar da kan al’umma.
- Ɗan Shekaru 15 Ya Kashe Wani Matashi Kan Rikicin Gona A Jigawa
- Zhao Leji Da Wang Huning Sun Gana Da Shugaban Majalisar Dattijan Kasar Madagascar
Ilelah ya kasance gogaggen manomi da ya taimaka sosai wajen bunƙasa harkar noma a Bauchi.
Ya yi aiki da gwamnati a matsayin manajan shirye-shirye na hukumar bunƙasa aikin noma ta jih5ar Bauchi (BSADP) kafin ya yi ritaya.
Har ila yau, a ranar Talata kafin rasuwarsa, ya jagoranci taron ƙaddamar da aikin gyaran majalisar dokokin Jihar Bauchi a matsayin mai gabatar da shirin.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Bauchi, Mukhtar Gidado ya fitar, ya bayyana marigayin a matsayin masani a harkar hulɗa da jama’a kuma ma’aikacin gwamnati na gari da ya bayar da gagarumar gudunmawa ga jihar.
Ya ce aikin wayar da kai da ya yi ba za a manta da shi ba.
Gwamna Bala Muhammad, ya bayyana jimaminsa bisa rasuwar tare da miƙa ta’aziyya ga iyalansa, abokansa da masarautar Bauchi.
Ya bayyana Ilelah a matsayin mutum mai kishin ƙasa da jajircewa a bakin aiki.
Ya roƙi Allah ya gafarta masa, ya jiƙansa kuma ya sanya shi a Aljanna Firdausi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp