Babban Asibitin Ƙasa da ke Abuja ya tabbatar da mutuwar wasu marasa lafiya biyu bayan samun mummunan yanayin rashin lafiya da ake zargin yana da alaƙa da allurar Fortcef (Ceftazidime), lamarin da ya sa asibitin tsananta sanya idanu kan amfani da maganin.
A cewar wata takardar sanarwa ta cikin gida mai kwanan watan 10 ga Satumba, 2026, wadda Daraktan Ayyukan Asibiti kuma Shugaban Kwamitin Ba Da Shawara Kan Kiwon Lafiya, Dakta O. Lawal, ya sanya wa hannu, Kwamitin Kula Da Illolin Magunguna na asibitin ne ya gano wannan matsala.
Sanarwar ta bayyana cewa marasa lafiyar biyu da suka mutu manya ne, kuma yanayin lafiyarsu yana da inganci kafin a yi musu allurar. Sakamakon haka, asibitin ya umarci dukkan sashi-sashin asibitin da su ƙara sanya idanu kan maganin Ceftazidime da aka sayo daga waje, musamman allurar Fortcef mai nauyin gram 1 (1g).
Rahoton ya nuna cewa maganin da abin ya shafa yana ɗauke da lambar rukunin ƙerawa (batch number) PEZIE001, wanda aka sarrafa a watan Mayun 2025 kuma zai daina aiki a watan Afrilun 2028, tare da lambar rajistar NAFDAC mai lamba C4-0247.
A ƙarshe, asibitin ya bayyana cewa ya riga ya miƙa rahoton faruwar lamarin ga Hukumar Kula Da Ingancin Abinci Da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC), tare da umartar likitoci da jami’an lafiya da su gaggauta bayar da rahoto a duk lokacin da suka lura da wata matsala da maganin ya haifar wa marasa lafiya.














