Iyalai da almajiran marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi sun tabbatar da cewa daga yau lamuran jagoranci na addini za su koma ƙarƙashin umarnin Khalifa Sharif Ibrahim Saley Al’husainiy, wanda aka amince da shi a matsayin shugaban Tijjaniyya a Nijeriya. Sun bayyana cewa biyayyarsu gaba ɗaya yanzu tana hannun Sharif Saleh, bisa ga irin kusancin da ke tsakaninsa da marigayin da kuma matsayin da take dashi a ɗarikar.
Babban ɗan marigayin, Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi, shi ne ya sanar da wannan mataki a yayin da tawagar Sharif Saleh suka kai ziyarar ta’aziyya a Bauchi. Ya ce tun kafin rasuwar Sheikh Dahiru ya yi musu wasiyya cewa Sharif Saleh ne zai jagoranci sallarsa kuma dole su yi masa biyayya a dukkan harkokin addini. Ya jaddada cewa jagoranci na ɗariƙa ba abin wasa ba ne, don haka sun miƙa lamuransu gaba ɗaya gare shi.
- Barau Ya Gargaɗi Gwamna Abba Kan Siyasantar Da Batun Tsaro A Kano
- Mace Aba Ce Mai Daraja, Ba Sai Ta Ba Da Kanta Ba Za Ta Yi Suna A Fim – Jamila Saleh
Sheikh Ibrahim ya kuma bayyana cewa su na buƙatar iznin Sharif Saleh a duk wani lamari da za su gudanar, domin ya kasance jagoran da marigayin ya yi musu nuni da shi. Ya ce dangantakar Sheikh Dahiru da Sharif Saleh ta addini da ta abota ta kai matakin da ba a iya misaltawa, wanda hakan ya sa biyayya gare shi ta zama wajibi ga mabiyan ɗarikar.
Tun da farko, babban limamin babban masallacin ƙasa, Farfesa Ibrahim Ahmad Makari, ya ce babu wanda zai ji zafin rasuwar Sheikh Dahiru kamar Sharif Saleh saboda tsananin kusancin da ke tsakaninsu. A matsayin tunatarwa, Sharif Saleh ne ya jagoranci jana’izar Sheikh Dahiru a ranar Juma’ar da ta gabata, abin da ya tabbatar da matsayin da marigayin ya ba shi tun kafin rasuwarsa.














