Wasu bayanai sun nuna yadda Ministar Ayyukan Jin-kai da aka dakatar, Betta Edu ta karbi Naira biliyan uku daga asusun COVID-19 na kasa domin ayyukan Jin-kai.
A wata wasika mai kwanan ranar 18 ga watan Satumba, 2023 mai lamba SH/145/A/220, Femi Gbajabiamila, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, ya shaida wa Edu cewa an amince da bukatarta na neman Naira biliyan uku daga asusun COVID-19.
- Kotun Koli: PDP Da APC Sun Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya A Nasarawa
- Mutane Kalilan Ne Suka Sace Dukiyar Nijeriya Ta Hanyar Tallafin Mai – Tinubu
“A sanar da ke cewar shugaban kasa ya amince da kashe N3,000,000,000.00 (Naira biliyan uku) daga asusun tallafa wa masu Covid-19 don tallafa wa ‘yan kasa,” Gbajabiamila ya rubuta.
Naira biliyan uku an raba wa kamfanoni tara ne ciki har da wanda ke da alaka da Olubunmi Tunji-Ojo, ministan harkokin cikin gida.
Sai dai ministan ya ce yayi murabus daga kamfanin a shekarar 2019.
Sai dai har yanzu babu wani cikakken rahoto da ke nuna yadda aka kashe kudaden.
Wannan na zuwa ne kimanin watanni biyu bayan Majalisar Tattalin Arziki ta Kasa (NEC), karkashin mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ta dakatar da shirin tallafin da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, bullo da shi sakamakon ayyukan almundahana.
Sai dai ana tunanin cewa tuni an yi sama da fadi da kudin ta hanyar amfani da hukumar NASSCO.
Amma NASSCO ta karin haske kan lamarin inda ta nuna ayyukan da ta yi game da kudaden.
“NASSCO da NBS suna aiki tare a bangarori da dama da suka shafi talauci, musamman a kan binciken inganta rayuw (NLSS).”
Idan ba a manta ba Shugaba Tinubu ya dakatar da Betta Edu kan zargin almundahana da wasu kudade a ma’aikatar Jin-kai.
Tuni EFCC ta fara gudanar da bincike a kanta bayan aike mata da sammaci zuwa ofishinta da ke hedikwatarta a Abuja.