Shugabannin al’umma na ƙaramar hukumar Kurfi a jihar Katsina sun cimma yarjejeniyar zaman lafiya da shugabannin ƴan bindiga da suka daɗe suna addabar yankin. An gudanar da wannan taro ne a dajin Wurma, ɗaya daga cikin wuraren da rikicin ya fi ƙamari, ƙarƙashin jagorancin Maraɗin Katsina kuma Hakimin Kurfi, Alhaji Mansur Amadu Kurfi, tare da shugaban ƙaramar hukumar, Hon. Babangida Abdullahi Kurfi.
A yayin taron, Hakimin Kurfi ya bayyana wannan mataki a matsayin sabon babi ga al’ummar Kurfi, yana mai jaddada cewa an zaɓi hanyar zaman lafiya domin ci gaban yankin. Ya kuma shawarci shugabannin ƴan bindigar da su kafa shugabancin gargajiya a tsakaninsu domin tabbatar da ɗawainiya da gaskiya.
- Hare-hare: Adadin Mutanen Da ‘Yan Bindiga Suka Kashe A Katsina Ya Haura 50
- Gwamnan Katsina Ya Dawo Gida Domin Ziyara Ga Al’ummar Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Wa Hari A Malumfashi
Shugabannin ƴan bindiga kamar su Alhaji Usman Kachalla Ruga, da Sani Muhindinge, da Yahaya Sani (Hayyu), da Alhaji Shu’aibu sun yi alƙawarin daina kisan mutane, satar shanu da garkuwa da mutane. Sun tabbatar da cewa manoma za su iya komawa gonakinsu cikin kwanciyar hankali tare da alƙawarin sako mutanen da suke tsare da su.
Shugaban ƙaramar hukumar, Hon. Abdullahi, ya bayyana farin cikinsa kan wannan mataki, yana mai cewa Kurfi ya shiga sabon zamani na ci gaba. Ya kuma tabbatar da cewa gwamnati za ta gyara makarantu da asibitoci tare da tabbatar da adalci ga duk wasu da aka kama.
Wannan yarjejeniya ta sanya Kurfi ta zama ƙaramar hukumar ta biyar a Katsina da ta ƙulla sulhu da ƴan bindiga, bayan Jibia, da Batsari, da Safana da Danmusa, abin da ya haifar da sabon fatan samun zaman lafiya mai ɗorewa zai dawo yankin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp