Mutane a garin Maru da ke Jihar Zamfara na cikin jimami bayan samun rahoton cewa limamin garin, Alkali Salisu Suleiman, da ‘ya’yansa biyu da jikansa sun mutu a hannun ‘yan bindigar da suka yi garkuwa da su.
Wata mata da ta kuɓuta daga hannun ‘yan bindigar ta dawo garin kwanan nan, inda ta shaida wa al’umma cewa limamin da wasu daga cikin iyalansa sun mutu.
- ‘Yansanda Sun Kama Masu Garkuwa da Mutane 12 Da Masu Sayar da Makamai 3 A Taraba Da Kaduna
- ‘Yan Ta’adda Sun Hallaka Mutum 8 Da Bam A Borno
Ta ce ‘yan bindigar sun sace mutane tara a dangin limamin, kuma har yanzu ana neman guda biyar daga cikinsu.
Alkali Suleiman, tsohon alƙalin kotun Shari’ar Musulunci ne, kuma an sace shi ne watanni biyu da suka gabata a wani hari da ‘yan bindiga suka kai, inda suka sace sama da mutum 20, ciki har da wani ango da amarya.
A lokacin da aka sace shi, an ce limamin yana fama da rashin lafiya, inda ‘yan uwansa suka kai masa magani da kaya kamar yadda ‘yan bindigar suka buƙata.
Babu tabbacin ko ya rasu sakamakon rashin lafiya ko kuwa an kashe shi.
An ce ‘yan bindigar sun fara neman Naira miliyan 20 a matsayin kudin fansa, amma iyalansa sun iya haɗa Naira miliyan 11 ne kacal.
Sun kuma buƙaci sabon babur da kayan abinci, duk a matsayin kuɗin fansa.
Bayan da matar da ta tsere ta shaida wa jama’a abin da ya faru a ranar Litinin, sai aka yi masa sallar jana’iza a ranar Talata kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Rundunar ‘yansandan Jihar Zamfara, ta bakin kakakinta DSP Yazid Abubakar, ta ce har yanzu ba ta samu labarin tabbacin mutuwar limamin da iyalansa daga hukumomi ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp