A yau ne kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana a taron manema labarai cewa, a baya-bayan nan, kungiyoyin masana da na fararen hula 34 na Amurka sun aike da wasika cikin hadin gwiwa ga shugabannin kasashen Amurka na Sin, inda suka bayyana ra’ayi mai ma’ana wajen inganta hadin gwiwa tsakanin Sin da Amurka, wanda ya yi daidai da kira ta gaskiya daga dukkanin sassan Amurka ga zaman lafiya da kyautata dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka, kana kasar Sin da Amurka su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu a matsayinsu na manya kasashe. Duk yadda al’amari ya canza, mahangar tarihi ta zaman lafiya tsakanin Sin da Amurka ba za ta canza ba, kana fatan jama’ar kasashen biyu na yin musaya da hadin gwiwa ba za ta canza ba, kuma fatan al’ummar duniya gaba daya na ci gaba mai dorewa game da dangantakar Sin da Amurka ba za ta canza ba.
Game da rasuwar tsohon sakataren harkokin wajen Amurka Henry Kissinger, Wang Wenbin ya ce, al’ummun kasar Sin za su tuna da sahihancin yunkurin Dr. Kissinger da gudummawa masu muhimmancin da ya bayar ga dangantakar Sin da Amurka. (Mai fassara: Yahaya)