An bude taron kolin mata na duniya a birnin Beijing a jiya Litinin 13 ga watan Oktoban nan. Yayin bikin bude taron, bangaren Sin ya yi kira ga dukkan bangarori da su sake tunawa da manufar da aka cimma a taron mata da aka gudanar a Beijing a shekarar 1995, don hanzarta cikakken ci gaban mata a duniya, ta hanyar cimma matsaya daya mafi girma, da fidda hanyoyi masu fade da aiwatar da matakai masu inganci.
Sin ta kuma gabatar da wasu sabbin shawarwari da ra’ayoyi. Wakilai daga kasashe daban-daban sun bayyana shawarwarin Sin a matsayin matakin dake ba da jagoranci wajen hanzarta sabon tsarin samar da cikakken ci gaban mata ta yadda za ta zama abun koyi ga saura.
Ministar ma’aikatar daidaiton jinsi, yara da kare jama’a ta kasar Ghana Dr. Agnes Naa Momo Lartey, ta jinjinawa kasar Sin, bisa jagorantar ayyukan hade dukkanin sassan shugabannin kasashe, don cimma burin bunkasa ci gaban mata da daidaiton jinsi.
Ta ce shawarwari hudu da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gabatar, duk suna kira ne da a yi hadin gwiwa don tabbatar da daidaiton jinsi, ya zama bai daya cikin manyan batutuwa da ya dace a tattauna a duniya. Ana bukatar karin ayyuka, kuma ba shakka wannan taro yana da matukar muhimmanci.
A nata bangare kuwa, wakiliyar kasar Tanzaniya Juliana Kibonde, cewa ta yi, an saurari jawabin shugaba Xi Jinping, wanda ke da matukar muhimmanci ga kasashen Afirka. An kuma lura da yadda za a ba mata ikon ci gaba a fannoni kamar na fasaha, da siyasa da sauyin yanayi. Kazalika, shugaba Xi ya ambaci batun gibin dijital, kuma ana iya fahimtar cewa, wasu kasashe suna da matakin dijital mai girma. Don haka kasashen Afirka na bukatar hadin kai don ciyar da fasaha gaba, ta yadda mata za su samu shiga ciki. (Amina Xu)