Gwamnatin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatoci jihohi da sauran kasashen duniya su tallafa wa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa birnin Maiduguri na Jihar Borno.
Wannan na zuwa ne bayan wata tawaga da gwamnatin Kano, ta tura jihar wadda ta bayar da gudunmuwar Naira miliyan 100 a madadin Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, domin tallafa wa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Jihar Borno.
- Bukukuwan Mauludi: Wani Mummunan Hatsari Ya Ci Rayukan Mutane 40 A Saminaka
- Kofin Gwamna Uba Sani: Ahmed Musa Ya Yi Alƙawarin Fitar Da ‘Yan Wasa 6
Tawagar gwamnatin jihar, karkashin jagorancin Kwamishiniyar Agajin Gaggawa da yakar Talauci, Hajiya Amina Sani da takwaranta na Yada Labarai Baba Dantiye ne, suka mika wa Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum cakin tallafin.
A ziyarar da su kai fadar gwamnanti a Maiduguri, Dantiye, ya bayyana alakar da ke tsakanin jihohin Kano da Borno.
Da yake mika sakon jajen gwamnatin Kano a madadin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya jajanta wa wadanda abin ya shafa, inda ya bayyana lamarin a matsayin wani babban Iftila’ina jin-kai.
Har wa yau, ya yi kira da a tallafa wa mutanen da abin ya shafa.
Wakilin gwamnan ya ce gwamnan Kabir na jaddada goyon bayansa ga al’ummar Maiduguri tare da tallafa musu a kowane lokaci.
Ya ce irin wadannan masifu na bukatar taimakon hadin gwiwa.
Ya yi addu’ar Allah Ya jikan wadanda suka rasu a sanadin ambaliyar, ya kuma yi fatan samun sauki ga wadanda suka jikkata.