Attajirin dan kasuwar nan na Jihar Kano, Alhaji Aminu Dantata ya bayar da tallafin Naira biliyan 1.5 domin taimakon mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.
Dantata, ya bayar da wannan tallafi ne yayin ziyararsa zuwa gidan gwamnatin Jihar Borno da ke Maiduguri a ranar Talata, tare da wata tawaga daga Jihar Kano.
- An Masa Daurin Watanni 4 Kan Satar iPhone Guda 2
- Kasar Sin Ta Lashe Gasar Fasaha Ta Duniya Karo Na 47
A yayin ziyarar, Dantata ya mika ta’aziyyarsa ga Gwamna Babagana Zulum da mutanen Borno, musamman wadanda suka rasa ‘yan uwansu a sakamakon ambaliyar.
Dattijon mai shekara 96 ya bayyana damuwarsa kan matsalar tattalin arzikin kasar nan, inda ya yi kira ga shugabanni da masu kudi su yi adalci sannan su yi tsoron Allah a harkokinsu.
Ya kuma yi addu’ar samun zaman lafiya mai dorewa a Borno da Nijeriya baki daya.
A nasa jawabin, Gwamna Zulum ya gode wa Dantata bisa wannan ziyara da kuma tallafin da ya bayar
Ya bayyana cewar mutanen Borno sun yi matukar jin dadin wannan kyauta.
“Babbanmu ya bayar da gudunmawar Naira biliyan 1.5 domin taimakon wadanda ambaliyar ta shafa. Allah Ya saka da aljanna. Mun gode, Baba,” in ji Zulum.
Wannan tallafin ya biyo bayan Naira biliyan daya da dansa, Alhaji Aliko Dangote, ya bayar domin taimaka wa wadanda ambaliyar ta shafa a jihar.