A kalla gawarwakin mutum 15 ne aka gano a kogin Ngadabul da ke birnin Maiduguri.
Ko’odinetan hukumar samar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) a Arewa Maso Gabas, Muhammad Usman, shine ya tabbatar da hakan a ranar Laraba a hirarsa da kamfanin dillacin labarai ta kasa (NAN) a Maiduguri.
Usman ya kara da cewa ana samun karuwar adadin mutanen da ambaliyar ruwa ke shafa da wadanda suke nutsewa a cikin kogi sakamakon ambaliyar ruwan a Maiduguri.
Ya gargadi iyaye da su tsawatar wa ‘ya’yansu domin ganin sun daina zuwa iyo ko wasan ruwa a kogi musamman a irin wannan lokacin da ake fama da damani domin kauce wa nutsewa ko shiga ruwan da ya fi karfinsu.
Usman ya cigaba da cewa kesa-kesan da ake samu na wadanda ambaliyar ruwa ke yi wa barnar a Arewa Maso Gabas abun damuwa ne matuka ainun.
“NEMA ta dukufa wajen fadakar da al’umma illar ambaliya da kuma matakan da ya dace suke dauka domin kariyan kai.
“Mun kuma gana da masu ruwa da tsaki daban-daban kan wayar da kan tare da samar musu da kayan tallafin gaggawa ga wadanda lamarin ya shafa,” a cewar Usman.
Kazalika, hukumar tsaron farin kaya ta NSCDC reshen Borno ta jibge jami’anta a iyakoki da gabar bakin kogin ruwa da domin hana yara shiga ruwa domin yin iyo ko wasan ruwa.