Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jihar Adamawa ya bai wa gwamnatin jihar Borno tallafin Naira miliyan 50 da jiragen ruwa guda shida domin tallafawa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a jihar.
A ziyarar da gwamna Fintiri ya kai Maiduguri, ya mika tallafin ga gwamna Babagana Zulum tare da rokon a kara tallafa wa al’ummar da abin ya shafa.
- Zaben Kananan Hukumomi: A Magance Maimaita Magudi A Jihar Kaduna
- Ya Kamata A Magance Shigar Banza A Masana’antar Kannywood -Samha M Inuwa
A cikin wata takarda mai dauke da sa hannun babban sakataren yada labarai na gwamnan, Humwashi Wonosikou a ranar Alhamis 12/08/2024, ya ce gwamnan ya bayyana nadamar asarar rayuka da dukiyoyin da aka yi, ya kuma bukaci gwamnatin tarayya da ta dauki matakin da ya dace domin shawo kan lamarin.
Musamman gwamna Fintiri, tare da takwaransa na jihar Borno, gwamna Babagana Umara Zulum, da kuma gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas, sun hau jirgin ruwan domin duba halin da ake ciki tare da jajanta wa ‘yan gudun hijira a jihar.
Gwamna Fintiri ya samu rakiyar sakataren gwamnatin jiha, Awwal Tukur, da ‘yan majalisar zartarwa na jihar, da abokan arziki.