Ya ku masu daraja, jama’ar jihar Kaduna da gwamnatin jihar Kaduna na yi imani wannan mukala za ta same ku cikin koshin lafiya. Na rubuto ne domin in bayyana damuwata matuka.
A matsayina na dan jihar da abin ya shafa da himmatuwa na wajen tabbatar da tsarin dimokuradiyya ya daidaitu a Nijeriya, dangane kuma da batutuwa da dama da suka shafi zaben kananan hukumomin da aka shirya gudanarwa ranar 19 ga watan Oktoban 2024 a jihar.
- Lallai Ƴan Nijeriya Suke Bibiyar Aiyukan Ƴan Majalisu – Shugaban EFCC
- Nazari Kan Dabarun Koyarwa Da Amfaninsu (5)
To duk wani mataki ko rashin daukar mataki da Majalisar Dokokin Jihar Kaduna (KDSHA) da kuma Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kaduna (KAD-SIECOM) za ta dauka, za ta shafi al’ummar jihar kai tsaye da kuma a kaikaice, da ‘yan takara a fadin jam’iyyu duka, da ma jihar baki daya. Wadannan abubuwan da nake so in ja hankali a kai, idan ba a magance su ba, tabbas za su gurgunta mutuncin tsarin zaben kuma a farko sun ta’allaka ne kan batutuwa da dama da suka hada da gaskiya, rikon amana, samun dama, kyawawan dabi’u da halayya, wadanda suke da matukar muhimmanci a kowane lokaci da kuma fanni na dimokuradiyya da kuma wanzar da amincewar jama’a kan harkokin zabe.
Da farko dai na damu matuka da yadda dokar zabe da majalisar dokokin jihar Kaduna ta yi wa kwaskwarima ba a bayyana wa jama’a ba. Ya zuwa yanzu dai kokarin da aka yi na saye ko samo kwafin ya ci tura kamar yadda kuma babu wata jam’iyyar siyasa a jihar da ta samu kwafin a halin yanzu sai dai ba mamaki ko shakka watakila ita jam’iyyar da ta samu kanta a kan madafun iko a jihar ta na da shi. Rashin bayyanai irin wannan takarda mai mahimmanci yana da ban tsoro, da damuwa,da tararrabi da haifar da tambayoyi masu mahimmanci game da gudanar da gaskiya a lokacin zaben, shigar da jama’a a cikin tsarin zabe da kuma sahihancin gyare-gyaren, saboda ya hana ‘yan kasa da masu neman takara samun cikakkiyar fahimtar dokokin da za a gudanar da zabe da dokokin gudanar da al’amuran Hukumar KAD-SIECOM.
Bugawa da samar da dokar da aka gyara kafin zabe shine mafi mahimmanci, don tabbatar da ka’idojin suna bayyanai kuma a bude, ka’idodin dimokuradiyya na hada kai da kuma ba da gaskiya kamar yadda aka tanada a Babi na 2, Sashe na 14 (1), da Sashe na 14 (2) (a), da Sashe na 14(2)(c) da sashe na 22 na kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999 da aka yi wa kwaskwarima. Bugu da kari, Dokar ‘Yancin Bayani ta 2011 (wato Freedom of Information Act) ta ba da garantin samun dama ga bayyanai, gami da irin takarddun kamar Dokar Zabe.
Abu na biyu kuma, wani lamari mai daure kai, shi ne na sanya kudin tsayawa takara da hukumar KAD-SIECOM ta yi kan fam din tsayawa takara. Ana biyan wadannan kudade ne ba tare da wata hujjar doka ba, musamman idan Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ba ta caji ‘yan takara irin wannan kudin fom a matakin kasa ba. Wadannan mun gani a zabukan 2023 inda gwamna mai ci da daukacin ‘yan KDSHA ba su biya wa INEC ko kwabo ba don neman tsayawa takara, ba su kuma ba INEC takardar shaidar biyan haraji ba. Idan aka yi la’akari da irin halin kuncin da ‘yan Nijeriya da dama ke fuskanta a halin yanzu, da suka hada da tsadar rayuwa, hauhawar farashin kayayyaki, da karancin man fetur da dai sauransu, tabbas wadannan kudade za su kawo cikas da raunin gwiwa a wajen fitar da ‘yan takara masu ingancin da cancanta, masu amana, amma saboda karancin kudi zai hana su shiga zaben. Bugu da kari, wannan doka rashin adalci ne da rashin sanin ya kamata a fili. Ina neman karin haske kan dalilan shari’a game da wadannan dokoki domin da alama ya saba wa sashe na 42, karamin sashe na 1 da na 2 na kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999 kuma ina kira ga KAD-SIECOM da ta sake duba wannan lamari domin tabbatar da daidaiton a fili ga dukkan ‘yan takara.
Na uku, idan aka yi la’akari da yiwuwar fuskantar kalubalen shari’a ko rashin amincewar jama’a da za su taso daga batutuwan da aka ambata a sama, alkawari da kudurin hukumar KAD-SIECOM na samar da daidaito ga duk wanda zai fafata a zabukan da ke tafe yana da ‘yanci, zai tarar da adalci da gaskiya ba tare da la’akari da halin zarafin kudi na ‘yan takarar ba da kuma tabbatar da cewa tsarin zaben ya yi daidai da dabi’un dimokuradiyya, to yana da matukar muhimmanci ga tsarin da dukkan masu ruwa da tsaki za su dauka a matsayin halaltacce don kaucewa da rusa kwarin gwiwar jama’a .Hakan zai tabbatar da cewa ba a karya sashe na 14,17 da 42 na kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999 da aka yi wa kwaskwarima ba.
Shawara ga KAD-SIECOM, ya kamata ta magance wadannan matsalolin a cikin gaggawa da suka cancanta. Tun da yake tabbatar da bayyane, adalci, da kuma samun zarafin yin zabe hakki ne na doka kuma harma hakki ne na kyawawan halaye da dabi’u.
A lura cewa KAD-SIECOM, Hukumar Korafe-korafen Jama’a (wato Public Complaints Commission), Majalisar Shawarar Jam’iyyu (IPAC), Taron Jam’iyyun Siyasar Nijeriya (CNPP) da Kungiyar ‘Yan Jarida na da babban rawar da za su taka a nan.
A karshe, maimaituwar fasalin magudi a Jihar Kaduna, ba shi da wata fa’ida ko alfanu ga duk wani dan Nijeriya mai hankali, madaidaicin tunani kuma mai kishin kasa, sai dai ga wadanda muke ganin ba su da hikima da hankali ko na miskala zaratun!